Zargin Ɗura Ashar Ya Kai Ga Wani Malamin Jami’a Zaman Gidan Yari A Kano

122

Kotun majistret mai zamanta a Rijiyar zaki ta aike da wani malamin jami,a gidan gyaran hali bisa zargin ɓata suna da cin mutunci.

Tun da farko ƴansanda ne su ka gurfanar da wannan lakcara mai suna Mustapha Hashim Kurfi wanda wani mai suna Abba Musa yayi ƙorafi akan sa.

Ƙunshin tuhumar ya bayyana cewar Abban yayi korafin cewar lakcaran ya duddura masa ashariya da shi da ƴan uwansa ta wayar tarho harma Abban ya naɗi muryar malamin yana ta runtuma ashar koda yake malam Mustapha Hashim Kurfi ya musanta zargin .

Barrister Ma’aruf Muhammad Yakasai shi ne lauyan da yake kare Mustapha Hashim ya kuma roki kotun da ta sanya shi a hannun beli kasancewar akwai dangantakar auratayya tsakanin mai kara da wanda ake kara.

Sai dai mai gabatar da ƙara Yusuf Saleh yayi su ka inda yace da zarar an bayar da belin Mustaphan zai haifar da tarnaki ga binciken ‘Yansanda.

Mai Sharia Aminu usman Fagge ya sanya ranar 19 ga wannan watan dan bayyana matsayar kotun ya kuma yi umarnin a tsare malamin zuwa waccan rana.

Rahoton Freedom Radio Kano

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan