Abba Ya Lashe Kyautar Ɗan Siyasar Da Ya Fi Farin Jini A 2019

1792

Wata Ƙungiyar Taimakon Kai da Kai mata dake jihar Kaduna, mai suna Kigo Matan Kwarai Cooperative Society, ta ba Injiniya Abba Kabir-Yusuf kyauta a matsayin ɗan siyasar da ya fi kowa farin jini a 2019.

Da take gababar da kashe-kashen kyaututtukan daban-daban a Bikin Raba Kyaututtuka na Shekara-Shekara, Shugabar Ƙungiyar, Hajiya Fatima Ladi ta ce Abba Gida-Gida ya cancanci a girmama shi bisa gudanar da kamfe cikin nasara da kuma sa matasa a cikin siyasa ba tare da tashin hankali ba a zaɓen 2019.

Ta ce Abba Gida-Gida ya cancanci kyautar bisa kasancewa ɗan takarar gwamna da ya fi farin jini a Arewacin Najeriya, wanda kuma ya zama abin tattaunawa a jihohi da dama.
A ta bakinta, da ya faɗi zaɓe, Mista Kabir-Yusuf bai harzuƙa goyon bayan da yake da shi ba, kuma hakan ne ya sa Kano ta samu zaman lafiya.

Waɗanda suka samu kyaututtukan daban-daban sun haɗa da Bunun Zazzau, Janar Sani-Sule ma ritaya da Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso.

Yayinda yake gababar da jawabinsa a yayin taron, Mista Kabir-Yusuf, wanda ya samu wakilcin Mai Magana da Yawunsa, Alhaji Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya ce tallafa wa mata shi ne wani kadarko da ya kamata a yi amfani shi don inganta walwala da rayuwar mata da ake ci da haƙƙinsu.

Kigo Matan Kwarai Cooperative Society ƙungiya ce ta mashahuran mata waɗanda ke ƙoƙarin inganta rayuwar mata a Arewacin Najeriya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan