Buhari Ya Sanya Hannu A Kasafin Ƙudin Shekarar 2020

47

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kasafin kudin shekarar 2020.


Mataimakin Shugaban ƙasa akan kafafen yaɗa labarai Femi Adesina ne ya bayyana hakan ne a shafinsa na fasebuk a yau Talata.


A watan Oktoban da ya wuce ne shugaban ya gabatar da daftarin kasafin kudin kasar na fiye da naira tiriliyan 10 a gaban zauren majalisar dokokin kasar nan.


Yayin da a farkon wannan watan majalisar dokokin kasar ta amince da shi a farkon watan nan.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan