Kwastam Ta Ƙwace Shinkafa ‘Yar Waje Mallakin Wani Aminin Buhari A Daura

296

Jami’an Border Drill Operations na Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta Ƙasa, NCS, sun ƙwace buhu 140 na shinkafa ‘yar waje, mallakin Alhaji Habu Sarkin-Fulani, wani hadimi kuma aminin Shugaba Muhammadu Buhari.

Shinkafar dai na ajiye ne a ɗakin ajiye-ajiye na Shugaba Muhammadu Buhari dake unguwar Fegi a Daura.

Mista Sarkin-Fulani aminin Shugaba Buhari ne, wanda yake karɓa da kuma kai kyaututtuka zuwa gare shi.

Majiyarmu ta tabbatar da cewa jamian na kwastam sun yi dirar mikiya ne a unguwar Fegi dake Daura, mahaifar Shugaba Buhari, sannan suka ƙwace shinkafar.

Majiyoyi sun ce an ba Shugaba Buhari kyautar shinkafar ne ta hannun Mista Sarkin-Fulani tun kafin a hana shigo da shinkafa ‘yar waje.

“Alhaji Sarkin-Fulani aminin Shugaba Muhammadu Buhari ne. Alhaji Sarkin-Fulani ba zai taɓa taɓa abinda ba nasa ba, koda kuwa zai lalace. Yakan ajiye duk wani abu da aka ce na Shugaban Ƙasa ne a ɗakinsa na ajiye-ajiye dake Fegi a Daura. Hatta gona da shanun Shugaban Ƙasa, Alhaji Sarkin-Fulani ne ke kula da su.

“Duk lokacin da Shugaban Ƙasa ya kai ziyara Daura, Mista Sarkin-Fulani yakan yi masa bayanin abubuwan dake cikin ɗakin ajiye-ajiyen, shi kuma (Buhari) sai ya faɗi yadda za a yi da kyaututtukan, ko yadda za a raba”, wata majiya a Daura ta shaida wa majiyarmu haka.

Lokacin da aka tuntuɓe shi don yin tsokaci, Mai Magana da Yawun Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta Ƙasa, Joseph Attah, bai amsa kiran da wakilin majiyarmu ya yi masa ba, bai kuma bada amsa ga rubutaccen saƙon dake neman ji daga hukumar, wanda da aka aika masa ba.

Jami’an kwatsam dai sun ci gaba da kai samame a ɗakunan ajiye-ajiye da kasuwanni tun lokacin da Najeriya ta hana shigo da shinkafa ‘yar waje a bara.

A makon da ya gabata, Ƙungiyar Manoman Shinkafa ta Ƙasa, RIFAN, ta roƙi Gwamnatin Tarayya da ta ci gaba da rufe boda don haɓɓaka tattalin arziƙin Najeriya.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan