Babu In Da Labaran Ƙarya Da Na Ɓatanci Su Ke Da Yawa Kamar A Najeriya – Sarki Sanusi II

286

Mai martaba Sarkin Kano Malam Sanusi II ya bayyana cewa babu in da labaran ƙarya da kalaman da su ke jefa kiyayya a tsakankanin al’umma kamar a ƙasar nan.

Sarkin ya bayyana hakan ne a gurin taron lakca akan LABARUN ƘARYA DA NA ƁATANCI A KAFAFEN YAƊA LABARAI DA SADA ZUMUNTA NA ZAMANI, wanda babban limamin masallacin juma’a na Ansarissunah, Sheikh Aminu Daurawa tare da shugaban Jami’ar Bayero Farfesa Muhammad Yahuza Bello su ka shirya.

Sarki Sanusi ya ce hakika abin takaici ne ganin yadda labaran karya da na batanci su ke kara karuwa a ƙasar nan. Ya ƙara da cewa a wasu lokutan wasu daga cikin jami’an gwamnati ne ke saƙa irin wannan labaran ƙaryar.

A ƙarshe Sarkin ya ja hankalin al’umma da su guji kitsa labaran ƙarya da kitsa kalaman da za su haifar da ƙiyayya a tsakankanin al’umma, ta hanyar jawo ayoyin daga cikin littafi mai tsarki da hadisai.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan