Kotu Ta Tabbatar Da Ƙarfin Ikon Ganduje Na Tumɓuke Sarakunan Kano

209

A ranar Talata ne Mai Shari’a A. T. Badamasi na Babbar Kotun Kano ya ƙi ƙara wa’adin umarnin wucin gadi da ya hana Gwamna Abdullahi Umar Ganduje daga tsoma baki a ikon masu naɗa sarki na Masarautar Kano.

A ƙara mai lamba K/197/2019, lauyan masu naɗa sarki ya roƙi kotun da ta ƙara wa’adin umarnin har zuwa lokacin da za a kammala sauraron ƙara.

Tasirin hukuncin na ranar Talata shi ne cewa a halin yanzu, Gwamna Ganduje yanan da ikon zartar da dukkan ikon da aka ba shi a Dokar Masarautun Kano ta 2019.

Wannan ya haɗa da ikon tumɓuke duk wani sarki da aka samu ya saɓa wa wani sashi na sabuwar Dokar Masarautun Kanon ta 2019.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan