Wata Ƙungiya Ta Buƙaci Ganduje Ya Tsige Sarki Sanusi

1227

Wata ƙungiya ta ƙalubalanci Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II da ya miƙa wuya ga hukumomin jihar Kano da Kundin Tsarin Mulki ya kafa don kawo ƙarshen turka-turkar da take tsakaninsa Masarautar Kano da gwamnatin jihar Kano.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai ranar Laraba a Ɗakin Taro na American Corner dake Ɗakin Karatu na Murtala Muhammad a Kano, ƙungiyar mai suna Concerned Civil Society Group, ta jaddada cewa ya zama wajibi Sarki Sanusi ya yi biyayya ga sabuwar Dokar Masarautun Kano, ko kuma ya fuskanci hukunci.

Ƙungiyar ta ce ta damu da ‘kawo cikas da cece-ku-ce na bai gaira ba dalili’ da Sarki Sanusi ke yi, ta buƙaci cewa ya kamata gwamnatin jihar Kano ta yi amfani da hukunci a kan duk wani mutum da zai iya kawo tangarɗa ga zaman lafiyar Kano.

Shugaban Ƙungiyar, Ibrahim Ali, wanda ya tattauna da manema labarai, ya jaddada cewa, indai Sarki Sanusi bai girmama sababbin dokokin masarautun ba, abubuwan da yake yi da turjiyarsa ka iya kawo tarnaƙi ga ikon da Kundin Tsarin Mulki ya ba gwamnatin Kano.

“Ya kamata Sarkin Kano ya mika kansa ga hukumomi jihar, saboda hakan ne zai kawo ƙarshen kiki-ka-kaka da haifar da cece-ku-ce da ake samu a halin yanzu”, in ji Mista Ali lokacin da yake ƙarin haske game da buƙatun ƙungiyar.

“Idan Sarkin Kano ya ƙi miƙa wuya ga gwamnatin jihar Kano, muna kira ga gwamnan jihar Kano da ya yi aiki da tanadin da Dokar Masarautun Kano ta 2019 ba sani ba sabo don ciyar da jihar gaba.

“Abinda Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ke yi yana ci gaba, kuma yana yin ƙafar angulu ga tabbatattun hukumomin gwamnatin jihar Kano da Kundin Tsarin Mulki ya kafa da sassanta, ba kawai ya saɓa da Kundin Tsarin Mulki ba, amma wani yunƙuri ne na ƙirƙirar wata jiha a cikin wata jiha, abinda ba wani shugabanci na ƙwarai da zai lamunta, ya bar shi ƙara zube”, in ji Mista Ali.

Turawa Abokai

2 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan