An Gano Macen Da Ta Shekara 6,000 A Duniya

121

Alamu sun nuna tana da duhun fata, gashinta ruwan kasa da shudin ido.
Wannan ce fuskar matar da ta rayu har tsahon shekaru 6,000 a duniya a yankin Scandinavia.

Sakamakon gatsa wani cingam da ta yi tun a shekarun baya, ya taimaka wa masana kimiyya wajen samun kwayoyin halittarta, wanda suka yi amfani da su wajen gano wace ce ita.

Wannan ne karon farko da aka gano kwayar halittar dan adam daga wani abu na daban wanda ba kashin halittar mutum ba, in ji wadanda suka yi binciken.

Alamu sun nuna tana da duhun fata, gashinta ruwan kasa da shudin ido.

Dr Hannes Schroeder na jami’a Copenhagen ya ce, “cingam din” an ciro shi ne daga jikin wata bishiya – abu ne mai daraja samun masaniyar kwayar halittar dan adam da ta dauki shekaru, musamman ta lokacin da ya kasance babu wani dan adan na karnin a raye.

“Abin al’ajabi ne a samu cikakkun kwayoyin halittar dan adam na shekaru daga wani abu da ba kashinsa ba,” ya ce.

Me muka sani game da ita?


Gano kwayoyin halittarta na gado dukkansu, ko kuma wadanda suke tattare da kashi, abubuwan da muka gani muka yi amfani da su don gano yaya kamanninta suke.

Kafataninta ta fi alaka da masu farauta da suke a nahiyar Turai sama da wadanda suka rayu a yankin Scandinavia a wancan lokacin, kamar dai su, tana da fata mai duhu, gashinta ruwan kasa da shudin ido.

Ana zaton ta fito ne daga tsatson wasu mutane ne da suka yi hijira daga yammacin Turai saboda zaizayewar kankara.

Yaya aka yi ta rayu?

Wasu kwayoyin halittar da aka kara bibiya sun bayar da haske kan rayuwarta a Lolland wani tsibiri a Denmark a kogin Balic. An kuma kara gano agwagwa da wani abin ci mai kamar gyada a matsayin abincin wancan lokacin.

“A wani yankin mai cike da manyan duwatsu a Denmark, bincike ya bankado cewa wasu mutane da suka zauna a yankin wanda suke binciko kayayyaki da dabbbobin daji, lokacin da aka fara noma da amfani da dabbobi a kudancin Scandinavia,” In ji Jensen da ke Jami’ar Copenhagen.

Kazalika masu binciken sun kara binciko wasu sinadaren halittar da ke damfare da cingam din da ta gatsa.

Sun gano sinadarin kwayar pathogens da kan iya haifar da cutar Nimoniya, da kuma wasu kwayoyin halittar da ke makale a baki, amma ba sa haifar da wata cuta.

Me wadannan bayanan ke shaida mana?


Masu binciken sun ce wadannan bayanan da aka samu ta wannan hanyar na nuna yadda mutanen baya suka yi rayuwarsu, da bayanai kan tsarin rayuwar kakannin kakanni da lafiaysu.

Kwayoyin halittar da aka gano daga cingam din sun bayar da haske kan yadda sinadarin Pathogens ya dauki shekaru cikin dan adam.

“Samun damar fito da irin wadannan kwayoyin halittar mutanen baya irin su Pathogen daga wani abin na daban ba karamain abin alfahari ba ne, saboda za mu iya karantar yaddda kwayoyin halittar suka samu a da, da kuma yadda suke a yanzu,” kamar yadda Dr Schroeder ya shaida wa BBC.

“Hakan ya shaida mana wani abu kan yadda suka bazu da kuma yadda suka samu.”

Rahoton BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan