A ranar Laraba ne Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da zaɓen gwamnan Legos, Babajide Sanwo-Olu, na Nasarawa, Abdullahi Sule, na Kaduna, Nasir El-Rufa’i da na Akwa Ibom, Emmanuel Udom.
Kotun Ƙolin ta kuma tabbatar da zaɓen Aminu Bello Masari na Katsina da kuma gwamnonin jihohin Ogun, Dapo Abiodun, Ebonyi, David Umahi da na Oyo, Seyi Makinde.
A wani hukunci da gaba ɗayan alƙalai suka amince da shi, Kotun Ƙolin ta tabbatar da cewa dukkan gwamnonin bakwai an zaɓe su a kan doran doka.
Da take tabbatar da zaɓen Gwamna Masari, Kotun Ƙolin ta amince da hujjojin lauya Lateef Fagbemi, SAN, cewa wanda ake ƙara na farko, Aminu Bello Masari, ya cancanta ya yi takara a zaɓen gwamna na ranar 9 ga Maris.
Kotun ta kuma yadda da Mista Fagbemi cewa mai ɗaukaka ƙara bai ƙalubalanci ainihin takardun Gwamna Masari ba, sai dai zarge-zarge cewa Gwamna Masari ya miƙa takardun ƙarya ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC don ta ba shi damar shiga zaɓen.
Mai Shari’a Mary Peter-Odili, wadda ta jagoranci babban hukuncin, ta tabbatar da cewa ɗaukak ƙara da Sanata Yakubu Lado ya yi ba ta da cancanta.
Saboda haka ne sai Mai Shari’a Peter-Odili ta tabbatar da hukuncin Kotun Sauraron Ƙorafe-Ƙorafen Zaɓen Gwamna da na Kotun Ƙolin, wadda ta tabbatar da zaɓen Gwmana Masari.
Kotun ta kuma yi watsi da ɗaukaka ƙara da ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Nasarawa, David Ombugadu ya yi, inda yake ƙalubalantar Gwamna Sule na jam’iyyar APC saboda rashin cancancta.
Haka kuma, a hukuncinta na gaba ɗaya, Kotun Ƙolin ta tabbatar da cewa ƙarar da Isa Hashiru, ɗan takarar gwamna na PDP a jihar Kaduna a zaɓen gwamna na ranar 9 ga Maris ya shigar, inda yake ƙalubalantar nasarar Gwamna El-Rufa’i na APC, ita ma ba ta cancanta ba.
Kotun ta tabbatar da zaɓen Gwmana El-Rufa’i.