Ganduje Ya Naɗa Mace A Matsayin Shugabar Ma’aikatan Kano Ta Farko A Tarihi

294

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya naɗa Binta Lawan Ahmed a matsayin Shugabar Ma’aikatan Kano, mace ta farko da ta samu wannan muƙami a tarihin jihar.

Majiyarmu ta ruwaito cewa har lokacin da aka naɗa Misis Ahmed, ita ce Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Ciniki ta Jihar Kano.

Wata sanarwa da aka raba wa manema labarai wadda Sakataren Yaɗa Labaran Gwamna Ganduje, Abba Anwar ya sanya wa hannu ranar Juma’a, ta ce naɗin zai fara aiki ne nan take.

Gwamna Ganduje ya bayyana sabuwar Shugabar Ma’aikatan a matsayin jajirtacciyar ma’aikaciya.

“Koyaushe takan yi aikinta a matsayin gogaggiya kuma jajirtacciyar ma’aikaciya, wadda ba ta burin da ya wuce ciyar da aikin gwamnati gaba”, in ji Mista Anwar.

Gwamnan ya kuma yabi tsohon Shugaban Ma’aikatan, Dakta Kabiru Shehu, wanda ya ci gaba da aiki a matsayin Muƙaddashi Shugaban Ma’aikata, bayan ya kammala shekarunsa na aiki.

“Dakta Kabiru Shehu ya yi ƙoƙari sosai. Ya kasance Shugaban Ma’aikata mai haba-haba da abokan aiki. Gaba ɗaya muna yi masa fatan alheri a gaba”, Mista Anwar ya ƙara da haka.

A cewar sanarwar, Gwamna Ganduje ya kuma naɗa Masu Bada Shawara na Musamman guda biyar, waɗanda su ma naɗin nasu ya fara aiki nan take.

Masu Bada Shawarar na Musamman su ne:

Ali Baba A Gama Lafiya- Mai Bada Shawara na Musamman Kan Harkokin Addinai
Mustapha Hamza Buhari Ba Kwana- Mai Bada Shawara na Musamman Kan Harkokin Siyasa
Hamza Usman Darma- Mai Bada Shawara na Musamman Kan Ayyuka na Musamman
Tijjani Mailafiya Sanka- Mai Bada Shawara na Musamman Kan Masarautu
Yusuf Aliyu Tumfafi- Mai Bada Shawara na Musamman Kan Al’amuran Jama’a.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan