Jami’an KAROTA Sun Damƙe Wani Ɗan Sandan Bogi

142

Jami’an hukumar da ke kula da zirga-zirgar ababen hawa a jihar wato KAROTA sun samun nasarar cafke wani matashi mai suna Aminu Muhammad dan unguwar Na’ibawa Ƴan Lemo, mai shekaru 33 da Babur din Adaidaita Sahu. Ɗauke da katin shaidar aikin Ɗansanda na A S. Alhaji mai muƙamin ASP.

Bayan tuhumar da jami’an hukumar ta KAROTA ta yi masa na mallakar katin shaidar aikin Dansanda(ID Card) da ba nasa ba, ya ce Dansandan abokinsa ne, kuma yana yin amfani da ID card din ne a matsayin shi ne a jikin hoton, wanda hakan ya sa shi karya dokar tuƙi akan titi saboda yana ɗauke da katin jabu.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya jami’an hukumar sun kama wasu da su ka yi sojan-gona da aikin Soji wadanda aka miƙa su hannun hukumomin da suka yi ƙarya da aikin nasu, bayan kammala bincike an tabbar Sojan-gona suka yi.

A ƙarshe hukumar KAROTA ta miƙa Aminu Muhammad hannun jami’an Yansanda domin a fadada bincike.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan