Majalisar Sarakunan Kano: Ganduje Ya Ba Sanusi Wa’adin Kwana Biyu

119

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II wa’adin kwana biyu ya karɓi ko ya yi watsi da muƙamin da ya ba shi na Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kano.

Wa’adin yana ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 19 ga Disamba, wadda Musa Yahaya Bichi, Babban Sakatare a Ofishin Ayyuka na Musamman ya sanya wa hannu a madadin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, SSG.

“Maigirma Zaɓaɓɓen Gwamna, yana buƙatar Maimartaba Sarkin Kano ya nuna KARƁAR ko AKASIN HAKA na muƙamin da aka ba shi a matsayin SHUGABAN Majalisar Sarakunan Jihar Kano kamar yadda wasiƙa mai mai lamba No SSG/REPA/S/A/86/T, mai kwanan wata 9 ga Disamba ta nuna.

“Ana buƙatar a sanar da maigirma gwamnan jihar Kano karɓar muƙamin ko akasin haka kwana biyu da karɓar wannan wasiƙa”, in ji wasiƙar.

A ranar 9 ga Disamba ne Gwamna Ganduje ya naɗa Sarki Sanusi a matsayin Shugaban Sabuwar Majalisar Sarakunan Jihar Kano.

Sabuwar Dokar Masarautun Jihar Kano, wadda a halin yanzu ake kotu game ita, ita ta samar da Majalisar Sarakunan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan