Sarkin Kano Sanusi II Ya Karɓi Matsayin Shugaban Majalisar Sarakunan Kano

353

Mai Martaba Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sanusi II ya karbi nadin da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi masa a matsayin shugaban majalisar Sarakunan Kano.

Sarki Sanusi ya aika wa Gwamnatin Jiha a rubuce cewa ya karbi wannan mukami kuma yana jiran umarnin gwamnatin domin sauran shirye shirye na fara zaman majalisar.

Tun da farko dai gwamnatin jihar Kano ta baiwa Sarkin na Kano wa’adin kwanaki biyu da ya yi bayanin karɓar wannan matsayi ko akasin haka.

Ita dai wannan majalisar Sarakunan ta hada da Sarkin Bichi, da Sarkin Rano, sai kuma Sarakunan Gaya da Karaye.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan