Farook Kperogi: Dan Ta’adda Da Biro?

  122

  Ko ka na son Farook Kperogi ko ba ka son sa, dole ka yarda marubuci ne mai hikima lokacin da ya fara shafinsa a jaridar Dailytrust kan adabin turanci ciki shekarar 2010.

  Shafin akwai kayatarwa kuma ya jawo masa ma su bibiyarsa da dama, wanda na kasance daga cikinsu. Amma da lokaci ya ja, ban sani ba ko girman kai ne ko shahara ko kuma rashin tarbiya ne, sai Farook ya fara cusa hancinsa cikin harkokin siyasa da cin mutuncin mutane wadanda ba su yarda da mahangarsa ba ko su ka ja da shi.

  Domin a san wane irin mutum ne shi, bari na fara kawo muku rigimarsa da wani dan jarida wato Phrank Shu’aibu. Farook ya zargi Phrank da satar fasahar shafinsa tare da ci masa mutunci.

  Bari ku ji daga bakin Phrank din da kansa a makalar da ya rubutu a jaridar Sahara Reporters ta ranar 1 ga watan Oktoba na 2012
  “Na yanke shawarar cewa ba abinda ya fi min a yanzu irin na shigar da Farook Kperogi kara kotu saboda sharrin da ya yi min na satar fasaharsa, bata min lokaci da kuma bata min suna”
  Ya ci gaba da kawo hujjojinsa da cewa “Shirin adabin turanci, ni ne na fara shi a shekarar 1996 a gidan talabajin na NTA, shekaru 14 kafin ya fara shaf insa” wato a shekarar da shi kansa Farook ke kamala karatun digiri na farko a jami’a Bayero, amma saboda rashin kunya ya ke zargin Phrank da satar masa fasaha.

  Phrank ya ci gaba da cewa “Hakika, ba a dauki wani lokaci ba kafin Farook ya janye zarginsa da yak e min ya fito karara ya nemi da in bashi kudi. Daga sannan na gane cewa Farook na amfani da matsayinsa na malamin jami’a wajen karbar kudi a hannun mutane.

  Ya turo min da wannan asusun ajiya na bankin UBA me lamba 04590680001597 da sunan SURAKATU IBRAHIM ya nemi in saka masa naira miliyan biyar a ciki” Kun ji daya daga cikin irin halin Farook Kperogi.

  Phrank ya nuna cewa ya kwakwalwar Farook ba ta ja, a matsayinsa na Farfesa domin ya kawo misalin wauta da rashin kwarewa a aikin jarida da ya yi a lokacin da ya buga wata mukala a jaridar Weeklytrust ta ranar 29th ga watan Satumba in da ya ke tambayar “Me ya kawo sunan jihar Mississippi a Abuja?” in da ya ci gaba da cewa “..Lokacin da na je hutu a Nigeria na gano wani titi a unguwar mawadata a Maitama Abuja wadda a ka sa wa suna Mississipi, ina dalilin saka wa wannan titi wannan suna?

  Mamaki na ya ta’azzara da na sake gano cewa babu wani titi a garin da a ka sakawa sunan wata jihar Amurka banda wannan. Shin mun rasa sunayen da zamu saka ne? idan mun rasa sunaye me zai sa mu rasa jihar da za mu dauko a Amurka sai wadda ta shahara a wajen gallazawa bakaken fata duk da mun kasance kasar bakaken fata mafi yawa a duniya? A yi min bayani don Allah”
  Phrank ya garzayo wajen yi wa wannan dakikin Farfesa bayani “Domin wayar da kan Kperogi, sunan Mississipi da a ka sakawa wannan titi ba sunan jihar da ke Amurka a ke nufi ba, a’a ana nufin Kogin Mississipi wanda ya ke jihar a Amurka domin an yi amfani da sunayen manyan koguna da ke nahiyoyin duniya wajen sakawa titunan suna kamar kogunan Nile, Amazon, da Ganges. Shin a matsayinsa na malami bai kamata a ce kafin ya buga wani abu a jarida sai ya yi tambaya, ko bincike kafin hakan?
  Hakika ina tausaya wa daliban da ya ke koyarwa a aji” Ni kaina na tausayawa ba dalibansa kawai ba har ma da wadanda ke bibiyar shafukansa a zaton malami ne mai ilimi irin wanda ya dace. Farook ya taba zama mai rubuta wa shugabansa bayani a lokacin mulkin Olusegun Obasanjo tsakanin shekarun 2002-2004.

  Ina zaton rashin samun hanyar karbar daloli na gwamnati shi ya saka shi fara neman kudade a hannun mutane irinsu Phrank.

  Kafin zaben 2015, Farook ya kasance yan gaba-gaba wajen yi wa Buhari Kamfe ta hanyar rubuce-rubucensa kuma ba na manta a lokacin da yan Buhari na kafofin sada zumunta su ka fito da taken FEBUHARI, kafin a dage zaben shugaban kasa na watan Fabrairu inda Farook ya wasa su kamar haka “Abin ya tafi da ni yadda aka yi amfani da adabi da iya zance wajen fitar da taken “FEBUHARI” da yan kafofin sada zumunta na kamfen din dan takarar jam’iyyar APC Muhammadu Buhari su ka yi.

  Hikimar ta isa ainun kuma ta fitar da basira da kayatarwa da ta jibanci lafazi, ma’ana, lokaci da amfani da yaren siyasa mai burgewa” Duk wannan yabo da Farook ke wasawa ba wani abu ba ne illa tsammani da fatan za’a biya shi idan Buhari ya ci mulki.

  Mai karatu kada ka dauka zancena hasashe ne kawai, bari na baku hujja. Lokacin da Farfesan namu ya tabbatar da cewa Buhari ya gama daukar masu bada shawara a kan harkar sadarwa kuma bai ga wata alama ta ana kokarin sakada shi koda a wani bangaren ba wanda ya tsammata ba, sai ya wasa wukarsa ya juya alkibla tare da far wa yan Buhari da gwamnatinsa ta ko’ina ya sami faka.

  Farmakinsa na farko shi ne a mukalarsa me taken “Sharudda 12 na yabon Buhari”. Ko kun san cewa a cikin jerin sharudda sha biyun da wanne ya fara? Bari na barshi ya fada da bakinsa “Ba yadda za’a yi ka nada masu bada shawwara 6 a fannin sadarwa sannan a ce mutum guda ka nada a matsayin mai baka shawara kan tattalin arziki” Maitar mayen ta fito fili a nan, domin abinda ke ba shi haushi shi ne a ce duk irin gwagwarmayar da ya yi ta rubuce-rubuce kafin zabe, bayan ga shi Farfesa a jami’ar Amurka sannan kuma wanda ya taba zama marubucin shugaban kasa, amma an dauki har mutane shida, amma babu shi a ciki.
  Wannan ne babban takaicinsa da kuma dalilinsa na zama abokin gabar Buhari da gwamnatinsa yadda ba ya ganin kowanne irin alheri na ta, sai dai lalubo nakasunta na gaskiya da na karya. Ba wanda zai manta lokacin da shugaba Buhari ya sami lalurar ciwon kunne ya tafi England neman magani, sai Farook ya dinga yada cewa gwamnatin tarayya ta kashe kimanin fam miliyan shida wajen biyan kudaden lura da ciwon.

  Lokacin da Garba Shehu ya fusata ya fito bainar jama’a ya ce Farook ya bashi kunya, ai kuwa sai mara kunyar ya kare kansa da cewa jaridar Banguard ce ta fara sakin labarin amma ya san cewa “Ni ne na farko da zan amince da cewa jaridar Banguard ba abar dogaro ba ce wajen sahihancin labarinta” Don Allah wane irin kwan-gaba-kwan-baya ne wannan? Ya na sane da haka ya ci gaba da yada labarin karya?

  Duk san da Kperogi ya sami damar muzanta APC, shugaban kasa ko magoya bayansa, ba ya daga kafa. Cikin mafi rashin imani, muni da abin kunya na irin wannan yada labaran karya game da gwamnatin Buhari shi ne na yada hotunan mafi shaharar jaruman Kannywood (Zaharadden Sani da Adam Zango), a matsayin sojojin Nigeria da aka kashe a harin barikin Metele a jihar Borno.

  Amma a na nuna masa wannan abu da yayi na nuna rashi tausayi, kishin kasa, sanin ya kamata da rashin kwarewa a aikin jarida, sai gogan na ku ya bi hanyar da ya saba wajen kare kansa. Ku ji abinda ya ke fada “Kafin na yada hoton na yi kokarin tantance hotunan abinda ya dauke ni zuwa wa su shafuka da a ka yada su a twitter…ban cika iya kallon munanan hotuna ba kuma hotunan sun fantsama a kafofin sadarwa shi ya sa na yarda cewa na gaske ne. Ni ban taba kallon fim din hausa ba kuma hoton ba ya da inganci daga inda a ka kwafo shi…mu a harkar aikin jarida an koyar da mu cewa hatta yakin basasar Amurka a shekarun 1860, hotuna na cikin abubuwan da su ka taimaka wajen karshensa”

  Don Allah ku ji irin dabbanci na wannan mutumin da ke kiran kansa Farfesa kuma a harkar jarida fa? Shin ya na son ya ce mana amfani da irin wannan hotuna na karya su ne za su kawo karshen mulkin Buhari kenan? Ko bai taba kallon fim din hausa ba (kada ku manta a Kano fa ya halarci jami’a) Adam Zango mawaki ne kuma mai talla, banda Ali Nuhu ba wanda fuskarsa ta shahara kamar ta sa a Kannywood.

  Wanda duk ya yi kokarin kalubalantar Kperogi a shafinsa a kan wani abu tare da hujja mai karfi sai kawai ya toshe shi daga shafin. Shin a matsayin Buhari na shugaban kasa da ya na so ba zai iya saka duk wata jarida a Nigeria, ta hanyar lallashi ko tursasawa, da ta daina daukan labaran Kperogi ba? Amma ya kyale shi ya yi ta tsula tsiyarsa amma saboda shi wanzami ba ya son jarfa, da zarar wani ya kalubalance shi sai ya toshe shi daga shafinsa.

  Ku ji abinda ya ke ikirari da bakinsa “Zan ci gaba da toshe duk wani mai goyon bayan gwamnati da ya ke da toshashshiyar kwakwalwa” Wannan ne tsarin Farook Kperogi, kuma ba yanzu ya fara ba domin kusan shekara biyu da wani abu kenan ya toshe ni daga shafinsa.

  Duk da cewa Farook ba abokina ba ne amma mu na da abokai iri daya tun na jami’a, domin mun yi Bayero tare kuma na fita da shekara daya a gabansa. Rikici na da shi ya samo asali a kan maganar furucin da magoya bayan Buhari na shafukan sada zumunci, wadanda a baya Farook ke yabonsu lokacin ya na tsammani sakamakon mukami, su ka fitar da ke nuna wadanda ba sa son Buhari wato “Wailing Wailers”.

  Kokarinsa na nuna dakikanci wadanda su ka fito da wannan taken ya sa na kalubalance shi. Cikin muhawarar mu sai ya kira da dakiki, domin shi a kullum yin zagi ko bakar Magana ko y atoshe ka, ba wani abu abu ba ne ga wanda su ke sa-in-sa da shi.

  Abin ya harzuka ni sosai yadda na mayar masa da martini da tunatar da shi cewa kada ya manta nima na je jami’a kuma na riga shi fita da shekara daya, kafin ya fara rubutu a jarida na riga shi da kyawawan shekaru hudu, kuma a matsayin dan jarida na sami karramawa daga jami’ar da ta fi kowacce jami’a a turai wato jami’ar Cambridge a matsayin dan jarida me rubutu da turanci kan harkar addini da kimiyya a shekarar 2008, haka kuma na sami wata karramawar da ga wata jami’ar dai a turai a shekarar 2015 da ke Austria, jami’ar Sigmund Freud, na rubuta daruruwan makaloli da gomman littafai, amma tunda shi a kullum da zuciyarsa ba da kwakwalwarsa ya ke tunani ba, ya kamata ya daina sukar kowa tunda ba zai iya jure a soke shi ba.

  Matsoracin Farfesan naku sai kawai ya toshe ni daga shafin nasa, don haka na fita harkarsa. A gaskiya ba don Farook na yi wannan rubutu ba domin na dauke shi jahilin-malami, na yi ne domin ya na da mabiya rubutunsa da shafukansa (a kalla ya na da mutane 10,000 a shafinsa na twitter) kuma yadda a ka doshi zaben 2019 idan mu ka zura ido wawayen mutane na fadar abinda su ka ga dama na jahilci da son rai ba tare da an nusar da jama’a ba, to hakika aikin mu na rubutu ya zama na banza kenan. Dole a rika bawa mutane abubuwa a faifai yadda za su iya dubawa su yi wa kansu alkalanci.

  Ali Abubakar Sadiq Ɗan Jarida Ne Kuma Mai Yin Sharhi Akan Al’amuran Yau Da Kullum. Ya Rubuto Daga Kano.

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan