Ganduje Na Shirya Wa Sarki Sanusi Sabuwar Kutungwila

1853

Duk da amincewa da karɓar shugabancin Majalisar Sarakunan Jihar Kano da ya yi, ta yiwu Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya faɗa cikin wasu sabbin matsaloli da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, a cewar rahoton jaridar Daily Trust Saturday.

Wata majiya dake da kusanci da gwamnatin jihar Kano ta labarta wa Daily Trust Saturday cewa duk irin martanin da Sarkin ya bayar ga wa’adin sa’o’i 48 da aka ba shi, wannan faɗa ka iya ci gaba.

A cewar majiyar, koda yake Sarkin ya amince ya zama Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar, gwamnati ka iya yin amfani da sharuɗɗan da ya gindaya a martanin da ya bayar don shirya masa kutungwila.

Wani sabon umarni daga gwamnatin jihar Kano zai buƙaci Sarki Sanusi ya riƙa neman izni a wasu harkokin gwamnati daga shugaban ƙaramar hukumar Kano Municipal, maimakon yadda aka saba shekara da shekaru, inda ake miƙa irin waɗancan buƙatu kai tsaye zuwa ga gwamna.

Haka kuma, dole Sarki Sanusi ya amince da zaman ofisoshin sauran sarakuna huɗu masu daraja ta ɗaya na Gaya, Rano, Ƙaraye da Bichi, ofisoshin da za a kafa a harabar Gidan Makama, wato a ƙarƙashin masarautarsa.

A jiya Daily Trust Saturday ta gano cewa gwamnatin jihar Kano ta fito da waɗannan shirye-shirye ne don canza tsarin sadarwa tsakanin gwamnatin jihar da Masarautar Kano, ta kuma ƙirƙiri ofisoshi a tsakiyar masarautar Sarki Sanusi bayan da ta karɓi wasiƙar amincewa da karɓar shugabancin Majalisar Sarakunan Jihar Kano daga Sarkin.

Gwamnatin jihar, a cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 19 ga Disamba, ta buƙaci Sarki Sanusi da ya nuna ‘karɓa’ ko ‘akasin haka’ na muƙamin da ta ba shi na Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kano, kuma ana so martanin nasa ya isa zuwa ga Gwaman Abdullahi Umar Ganduje a cikin kwana biyu da karɓar wasiƙar.

A wasiƙar martaninsa, ita ma mai ɗauke da kwanan 19 ga Disamba, Sarkin ya bayyana amincewarsa ga gwamnan jihar.

Koda yake dai a bisa tsarin mulki, sarakunan gargajiya suna ƙarƙashin shugabannin ƙananan hukumominsu ne, abinda aka saba da shi tsawon shekaru musamman a jihar Kano shi ne Sarki yana mu’amala kai tsaye da gwamna.

“Sarkin ya yi magana game da samar da sakatariya da kuma sanar da sauran mambobin majalisar. Bari in faɗa maka, gwamnati za ta samar da sakatariyar, sannan ta samar da ofis ga kowane sarki daga cikin sabbin sarakunan da aka naɗa”, in ji majiyar.

“Kuma, gwamnati za ta bayyana a fili cewa duk lokacin da Sarki Sanusi yake son yin tafiya, dole ya nemi izini daga shugaban ƙaramar hukumarsa, wato Kano Municipal.

“Duk wani yunƙuri da Sarkin zai yi na ƙin yin biyayya ga waɗannan sharuɗɗa da ma sauran, za a zarge shi da rashin biyayya, kuma wannan kaɗai zai iya sa a tumɓuke shi”, majiyar ta ƙara da haka.

Majiyar ta ƙara da cewa an aika wa Sarki Sanusi wasiƙu biyu ne, inda ake buƙatar ya karɓa ko ya yi watsi da naɗin.

Majiyar ta tuna cewa wasiƙar farko da aka aika wa Sarkin ita ce ta ranar 9 ga Disamba, 2019, inda ya bada amsa ranar 12 ga Disamba.

A amsar farko da Sarkin ya bayar, kwafin wasiƙar da Daily Trust Saturday ta samu bai nuna Sarkin ya karɓi muƙamin ba ko kuma a’a, wani yanayi da ya haifar aka aika masa wasiƙa ta biyu, wadda aka ba shi sa’o’i 48 don ya bada amsa.

A amsarsa ta farko, a wasiƙar da Muƙaddashin Sakataren Majalisar Masarautar Kano, Alhaji Abba Yusuf ya sanya wa hannu, mai ɗauke da kwanan watan 12 ga Disamba, 2019, ta nuna cewa Sarkin ya bar Kano don yin wata ziyarar aiki, saboda haka ba zai iya bada amsa ba ga wasiƙar da gwamnatin jihar Kano ta aika masa.

“Maimartaba Sarkin Kano ya bar Kano don wata ziyarar aiki tsawon wannan mako. Maimartaba ya halarci taron tattaunawa na Majalisar Sarakunan Arewa a Kaduna ranar Litinin, 9 ga Disamba, 2019. Daga nan ya wuce Abuja inda ya halarci taron tattaunawa na Majalisar Sarakunan Najeriya ranar Laraba, 11 ga Disamba, 2019. A ranar Alhamis, 12 ga Disamba, 2019, Maimartaba ya halarci taron tattaunawa na Majalisar Harkokin Addinai ta Ƙasa, shi ma dai a Abuja.

“An umarce ni in sanar da kai cewa Maimartaba ya karɓi wasiƙarka, kuma ya lura da abubuwan da ta ƙunsa”, a cewar wasiƙar.

Idan dai za a iya tunawa, kafin Sarki Sanusi ya amince ya zama Shugaban Majalisar Sarakunan, an samu wasu ƙungiyoyin fararen hula da suka yi kira da a tsige shi, wasu kuma suka yi suka ga hakan.

Wani gungun ƙungiyoyin fararen hula 34, waɗanda ake zaton gwamnati ce ta ɗauki nauyinsu sun yi kira ga Gwama Ganduje da ya tsige Sarki Sanusi sakamakon rashin ɗa’a da yake nuna masa.

Gungun ƙungiyoyin, banda yin taron manema labarai a Ɗakin Taro na American Corner dake Ɗakin Karatu na Murtala Muhammad, sun kuma gabatar da buƙatarsu a rubuce ga gwamnan.

Sai dai ƙasa da sa’o’i 24, sai ga wasu ƙungiyoyin farar hula 183 sun fito, waɗanda su kuma ake tunanin Sarki Sanusi ne ya ɗauki nauyinsu, sun fitar da sanarwa, inda suka nesan ta kansu daga wancan kira na farko.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan