Ƙungiyar Dattawan Arewa Za Ta Yi Sulhu Tsakanin Ganduje Da Sarki Sanusi

280

Sakamakon damuwa da rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II bisa zargin bambancin siyasa, wanda ya haifar da raba Masarautar Kano mai ɗimbin tarihi zuwa gida biyar, Ƙungiyar Dattawan Arewa, NEF ta yanke shawarar tsoma baki a rikicin.

Majiyarmu ta ruwaito cewa tsoma bakin na NEF, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Ango Abdullahi ya zo ne tsaka da wata sabuwar rigima ta wa’adi da Gwamna Ganduje ya ba Sarki Sanusi bisa shugabancin Majalisar Sarakunan Jihar Kano.

Wa’adin dai yana ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 19 ga Disamba, wadda Musa Yahaya Bichi, Baban Sakatare a Ofishin Ayyuka na Musamman ya sanya wa hannu a madadin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, SSG.

“Maigirma Zaɓaɓɓen Gwamna yana buƙatar Maimartaba Sarkin Kano ya nuna KARƁAR ko AKASIN HAKA a kan muƙamin da aka ba shi na SHUGABAN Majalisar Sarakunan Jihar Kano, kamar yadda wasiƙa mai lamba No SSG/REPA/S/A/86/T, mai ɗauke da kwanan watan 9 ga Disamba ta buƙata.

“Dole karɓar muƙamin ko akasin haka ta isa zuwa ga zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano kwana biyu da karɓar wannan wasiƙa”, in ji wasiƙar.

Koda yake wata wasiƙa da aka ce ta fito ne daga Masarautar Kano, wadda ke nuna cewa Sarki Sanusi ya karɓi tayin na gwamna ta bazu a soshiyal midiya, har yanzu abinda bai fito fili ba shi ne ko Sarkin ya amince ya shugabanci Majalisar Sarakunan, saboda har yanzu Masarautar Kano ba ta tabbatar da sakin waccan wasiƙar amincewa ba a hukumance.

A cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 15 ga Disamba, 2019, wadda aka aika wa Walin Kano, Mahe Bashir, Farfesa Abdullahi ya ce: “NEF ta damu matuƙa da yadda al’amura ke ɗaukar wani sabon salo a yanzu sakamakon irin rashin fahimtar dake tsakanin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da kuma Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II da kuma wani yanki na masu faɗa a ji a Kano.

“Rikicin, muna jin tsoro, yana ɗauke da wasu abubuwa da ba za a iya gani ba, waɗanda daga ƙarshe ke yin barazana ga mutuncin masarautar Kano gaba ɗaya, zaman lafiya da kuma samun zaman lafiya a yankin Arewa.

“A bisa wannan damuwa, Ƙungiyar Dattawan Arewa, ta yanke shawarar tattara mashahuran ‘yan Arewa, dattawa da dukkan nau’o’in shugabanni da masu ruwa da tsaki don tsoma baki da samun mafita ta ƙarshe a wannan al’amari”, a cewar wasiƙar da majiyarmu ta gani.

Farfesa Abdullahi ya ce za a yi taron sulhun ne a Tahir Guest Palace a ranar Lahadi, 22 ga Disamba, 2019.

“Yayin zamanta a Kano, tawagar za ta tattauna da dattawan Kano da manyan masu ruwa da tsaki, Sarki Sanusi da Gwamnan Kano.

“Ina so in sanar da kai cewa sakamakon muhimmancinka da irin muƙamin da kake da shi a Masarautar Kano, an zaɓe ka daga cikin manyan mutanen da tawagar za ta tattauna da su a ranar Lahadi, 22 ga Disamba, 2019, a Tahir Guest Palace Majestic Hall da ƙarfe 12 na rana.

“Fatanmu shi ne wannan tsoma baki zai gano tushen al’amarin, sannan ya kawo mafita ta ƙarshe tare da da mutunta juna da girmamawa don jihar ta ci gaba”, wasiƙar ta ƙara da haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan