Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Kusa Da Gidan Goodluck Jonathan

157

Maharan wadanda ba a tantance su ba sun kai harin ne kan wani sansanin soji da ke daf da gidan tsohon shugaban, ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan a garin Otouke na jihar Bayelsa.

Wata sanarwa da mai magana da yawun Goodluck Jonathan, Ikechukwu Eze ya fitar, ta ce maharan wadanda suka je garin a cikin kwale-kwale mai inji guda biyar sun far wa jami’an tsaron ne da misalin karfe 1:30 na daren Litinin.

Mutanen sun kai harin ne kan sansanin sojojin mai tazarar mita 100 da gidan Goodluck Jonathan, da manufar kwace jiragen ruwa mallakar sojoji.

To sai dai sanarwar ta ce sojojin sun samu nasarar fatattakar ‘yan bindigar bayan fafatawa.

Mista Ike ya kara da cewa soja guda daya ya rasa ransa sannan wani sojan ya samu raunuka inda yake asibiti domin karbar magani.

Mai magana da yawun tsohon shugaban ya ce lokacin da ake wannan artabu, mai gidan nasa ba ya gari amma kuma ya koma Otouke da sanyin safiyar Talata domin jajanta wa al’ummar garin kan abin da ya faru.

Rahoton BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan