Home / Labarai / Cin Zogale Ga Mata Masu Juna Biyu Na Da Matuƙar Illa Ga Jariran Da Ke Ciki – Bincike

Cin Zogale Ga Mata Masu Juna Biyu Na Da Matuƙar Illa Ga Jariran Da Ke Ciki – Bincike

Duk da cewa zogale ganye ne dake dauke da sinadarai daka samar wa mai ci lafiya da kuma kare shi daga kamuwa da cututtuka. Hakan kuwa bai hana binciko wasu illolin da ke tattare da cin shi ba musamman ga mata masu juna biyu.

Ganyen zogale na taimaka wa wajen kawar da hawan jini, cututtukan dake kama zuciya, ciwon suga, cutar daji, inganta fatar mutum da dai sauransu.

Sai dai kash! Duka amfanin da zogale ke da shi a jiki, ma’abota bincike daga jami’ar Ibadan sun yi kira ga mata masu juna biyu da su guji cin ganyen zogale, ‘ya’yan zogale da man zogale domin yana yi wa dan dake ciki illa.

Farfesa Adefolarin Malomo, Foluso Atiba da Dr Innocent Imosemi ne suka gano haka a binciken da suka gudanar a jikin wasu beraye 20 da ke dauke da ciki.

Sakamakon binciken ya nuna cewa ganyen Zogale na yi wa kwakwalwa, jijiyoyi da kasusuwan jaririn dake ciki illa matuka tun kafin ya zo duniya.

Malamo ya ce alamun illolin da Zogale ke yi wa jarirai sun hada da haifo dan da bashi da kafafuwa ko kunne ko baki ko cibiya sannan kuma da kasusuwa marasa karfi da dai sauran su.

Likitocin sun yi kira ga mata masu ciki da su hakura da cin ganyen Zogale a duk lokacin da suke dauke da ciki.

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Shugaban riƙon ƙwaryar gwamnatin ƙasar Chadi ya ziyarci Mohamed Bazoum

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwaryar kasar Chadi Janar Mahamat Idriss Deby lokacin da ya kai wa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *