JAMB Ta Bayyana Ranar Da Za A Fara Jarrabawar UTME Ta 2020

242

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu, JAMB, ta ce za ta gudanar da Jarrabawar Bai Ɗaya Ta Shiga Manyan Makarantu ta 2020, UTME 2020, daga 14 ga Maris zuwa 4 ga Afrilu, 2020.

Magatakardar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana haka yayinda yake karɓar baƙuncin Kwamishinonin Ilimi na Jihohi ranar Litinin a Abuja.

Mista Oloyede ya kuma ce JAMB za ta fara yin rijistar jarrabawar gwaji daga 13 ga Janairu zuwa 1 ga Fabrairu, 2020, yayinda za ta gudanar da jarrabawar gwajin ranar 18 ga Fabrairu, 2020.

Ya yi bayanin cewa haka kuma za a fara yin UTME ta 2020 da kuma Jarrabawar Neman Aji Biyu Na Manyan Makarantu a tare, daga 13 ga Janairu zuwa 17 ga Fabrairu, 2020.

A ta bakinsa, JAMB za ta shigo da Hukumar Bayar Da Lambar Shaidar Zama Ɗan Ƙasa, NIMC a UTME ta 2020 kamar yadda Majalisar Zartarwa ta Ƙasa, FEC ta umarta.

Daga nan sai ya yi kira ga ɗaliban da za su zana jarrabawar da su garzaya kowace Cibiyar NIMC don samun Lambar Shaidar Zama Ɗan Ƙasa, NIN don samun damar yin rijistar jarrabawar.

“Dole kowa ya tashi tsaye ya ƙarfafi NIMC. Za ma mu shigo da Hukumar Kula da Ƙwararru A Kwamfuta, CPRC, don ta taimaka wajen kula mana da Cibiyoyin Ɗaukar Jarrabawar ta Kwamfuta, CBCs.

“Kuma za mu amfana da Galaxy Backbone. A kowace Cibiyar Ɗaukar Jarrabawa, CBT, za a tanadi Cibiyoyin Yin Rijista na NIMC.

“A wani ci gaban, fiye da kaso 40% na ɗaliban sun samu Lambarsu ta NIN.

“Wannan zai sauƙaka mana aikinmu saboda waɗanda ba su iya yin rijista ba a yanzu za a iya tura su Cibiyoyin Rijista na NIMC a yayin yin rijista”, in ji Magatakardar na JAMB.

Magatakardar ya ƙara da cewa muhimmancin ɗalibi ya samu Lambar NIN shi ne kawar da matsalar yin rijista fiye da sau ɗaya, wadda ta zama matsala a yayin rijistar 2019.

“Gogewarmu ta bara ta nuna cewa wasu ɗalibai sun yi rijista fiye da sau ɗaya don su yi sojan gona. Muna sane da cewa maguɗin jarrabawa yana farawa ne tun a wajen yin rijista.

“JAMB tana buƙatar cikakken haɗin kan Kwamishinoni Ilimi na Jihohi don su taimaka wajen wayar da kan ɗalibai a jihohinsu daban-daban bisa buƙatar da muhimmancin NIN a rijistar 2020.

“Mun kira ku ne don mu sanar da ku game da shirye-shiryenmu na gudanar da UTME ta 2020, kuma ku mayar da hankali ga jarrabawar da gwamnati ke shiryawa a jihohinku, kuma ku kula da ƙaruwar cibiyoyin ɗaukar jarrabawa da ake buɗewa don maguɗin jarrabawa”, in ji Mista Oloyede.

Ya yi bayanin cewa hukumar ta tanadi Babban Tsarin Kula da Guraben Karatu, CAPS, da aka tsara don hana makarantu daga canza ko gabatar da wani shiri ko kwas ɗin da bai zaɓa ko ba ta zaɓa ba.

Ya ƙara yin bayanin cewa wasu makarantu sun fito da tsarin ba ɗalibai guraben karatu ba ta hanyar amfani da CAPS ba a shafukansu na Intanet, yana mai cewa duk wata makaranta da take yin haka tana jefa waɗannan ɗalibai a cikin haɗari a gaba.

Daga nan sai ya ce JAMB ta umarci makarantu su riƙa fifita kwasa-kwasan da ɗalibai ke zaɓa.

Game da labarin da ya karaɗe soshiyal midiya na wata ɗaliba, Goodness Thomas, wadda ta samu maki 302, amma Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, ABU, ta hana ta gurbin karatu, Mista Oloyede ya ce ba ta samu makin da ya kamata a ba ta gurbin karatu a kwas ɗin da ta zaɓa ba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa Misis Thomas ta nemi a ba ta damar karkata ‘Medicine’, amma sai jami’ar ta ba ta ‘Human Anatomy’.

“Jami’ar ta yi daidai da ta ba ta ‘Human Anatomy’. Ta yi ta uku ne daga Naija, jami’ar ta zaɓi ɗaliban farko guda biyu daga jihar tata, saboda haka ba ta cancanci ABU ta ba ta gurbin karatu ba”, in ji Mista Oloyede.

Turawa Abokai

2 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan