Saboda Tsoron Bulala Na Daina Zuwa Makarantar Islamiyya – Obasanjo

339

Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana ‘bulalar Malam’ a matsayin babban kalubalen da ya fuskanta wajen neman ilimin addinin Musulunci a yayin da yake zuwa makarantar Islamiyya.

Obasanjo ya bayyana hakam ne a lokacin wani taron ƙulla kyakkyawar dangantaka tsakanin Musulmai da Kirista da aka shirya a garin Abekouta da ke jihar Ogun, inda yace yana zuwa Islamiyya kullum a lokacin da yake yaro, amma yawan bulala yasa ya tsere.

A jawabinsa, Obasanjo ya yi kira ga al’ummar kasar nan da su zauna lafiya da junansa, tare da hada kai domin cigaban kasa. Ya ƙara da cewa da tuni ƙasar nan ta wuce haka idan da a ce Musulmai da Kiristoci sun zauna lafiya da junansu.

“Idan da a ce zamu zauna lafiya da maƙwabtanmu, a matakin unguwanni, jiha, ƙasa, nahiya da kuma duniyar gaba daya da mun samar da kyakkyawar duniya abar sha’awa. Bari ku ji, ina zuwa Islamiyya a kauyenmu domin a kauyenmu an hada Coci da Masallaci a wuri daya ne.

“Da nake yaro a kauyenmu babu wani bambanci, domin haka sai na fara zuwa makarantar Islamiyyah, amma babban abin da ya koreni daga Islamiyyah shi ne bulalar Malam, amma abin da na koya a kauye yayin da nake girma shi nake dabbakawa a rayuwana har yanzu.” Inji shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan