Sarki Sanusi Ya Sallami ‘Sokon Kano’ Daga Fada

440

Sarkin Kano, Muhammd Sanusi II ya hana Sokon Kano, Ahmadu Abdulwahab zuwa Fada.

Wannan mataki ya zo ne sa’o’i 24 bayan Kwamitin Sulhu na Kungiyar Dattawan Arewa, NEF, wanda tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Abdulsalami Abubakar ke yi wa jagoranci ya yi kira ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sarki Sanusi da su dakatar da ɗaukar duk wani mataki dake da alaƙa da ƙirƙirar sabbin masarautu a jihar.

An ce Sokon Kano ya yi wasu kalamai marasa daɗi a kan Sarki Sanusi a bikin yaye ɗalibai na Makarantar Koyon Aikin Ɗan Sanda dake Wudil, makon da ya gabata.

An ga wannan bafade a cikin wani faifan bidiyo da ya karaɗe soshiyal midiya yana yin kalaman a yayin taron.

Da yake tabbatar da al’amarin, Sokon Kano ya faɗa wa jaridar Daily Trust ta waya cewa jiya ne abin ya faru bayan da ya je Fada da safe.

“Na je Fada yau (jiya) da safe. Sai na shiga cikin sauran fadawa don raka Sarki zuwa Fada, amma ‘yan mintuna kaɗan bayan da Sarki ya zauna, sai Shugaban Ma’aikatan Sarkin, Alhaji Munir Sanusi ya tunkaro ni.

“Ya tambaye ni me yasa na zo Fada, na ce masa na zo yin aikina ne kamar yadda na saba. Daga nan sai ya sanar da ni cewa ba a buƙatar sake gani na a Fada, saboda ba zai yiwu in haɗa kai da maƙiyan Fadar ba, kuma a lokaci guda ina tare da Fadar. Daga nan sai ya umurce ni in bar Fadar, kuma kar in ƙara dawowa.

“Ina zaune, sai Shugaban Ma’aikatan Sarkin ya aika dogarin sarki zuwa Babban Dogari Mai Kula da Fada, DCO, ‘yan mintuna kaɗan bayan sun tattauna, sai DCO ɗin ya fito, ya umarce ni da in bar Fadar”, in ji shi.

Sokon Kano shi ne bafade na uku da Sarki Sanusi ya sallama tunda aka fara rikici tsakanin sa da Gwamna Ganduje.

Na farko da aka sallama shi ne Babban Sakataren Sarki, Alhaji Isa Pilot, sai Majasirdin Kano, Alhaji Auwalu Idi.

Ƙoƙarin jin ta bakin Shugaban Ma’aikatan Sarkin na Kano, Mista Sanusi bai yi nasara ba, saboda bai amsa kiraye-kirayen waya da aka yi masa ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan