Saudiyya Ta Haramta Aure Tsakanin ‘Yan Ƙasar ‘Yan Ƙasa Da Shekara 18

272

Ma’aikatar Shari’a ta Saudiyya ta haramta aure a tsakanin al’ummar ƙasar ‘yan ƙasa da shekara 18, kamar yadda ta sa shekara 18 a matsayin mafi ƙarancin shekarun da za a yi yin aure a ƙasar.

Ministan Shari’a Kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta Alƙalan Ƙasar, Dakta Walid Al-Samaani ne ya fitar da sanarwar ranar Litinin zuwa ga dukkan kotuna, inda ya jaddada haramcin aure a tsakanin al’ummar ƙasar ‘yan ƙasa da shekara 18.

Kafin wannan doka, auren ƙananan yara ya zama ruwan dare a Saudiyya, inda ake aurar da ɗaya daga cikin ‘yan mata bakwai kafin shekara 18.

Sai dai Ministan Shari’a na Saudiyyar na ƙoƙarin sauya abubuwa.

A takardar da aka fitar ranar Litinin, Ministan ya bada umarnin cewa duk wasu buƙatun aure dole a kai su kotuna na musamman don bin dokoki kamar yadda Dokar Kare Yara ta tanada.

Umarnin Mista Al-Samaani’s ya dogara ne da Sakin Layi na 16/3 na Dokar Kare Yara ta Saudiyya.

Dokar ta ce: “Kafin a ƙulla auratayya, mutum ya sani cewa auren ɗan ƙasa da shekara 18 ba zai yi masa ko mata illa ba, kuma za su iya cimma muradunsu, namiji ko mace”.

Wannan ba shi ne karon farko da Saudiyya ke yunƙurin hana aurar da ƙananan yara ba a ƙasar.

A watan Janairu, ƙasar ta amince da dokokin da suka haramta aurar da ‘yan ƙasa da shekara 15.

Haramcin ya biyo bayan wani hukunci da Majalisar Shura ta Ƙasar ta yi, wanda biyu bisa uku na mambobinta suka amince, a cewar jaridar Arab News.

Sai dai waɗancan dokoki suna da naƙasu kaɗan.

Ta ba yara da ba su kai 18 ba damar yin aure, idan sun samu izini daga kotu ta musamman.

Amma dokar ta ranar Litinin ta haramta aure tsakanin mutanen da ba su kai shekara 18 ba, ta kuma yi tanadin hukukce-hukunce ga masu kunnen ƙashi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan