Jaruma Halima Atete Za Ta Angwance A Sabuwar Shekara

709

FITACCIYAR jaruma Halima Yusuf Atete za ta yi aure a wannan watan mai kamawa na Janairu, 2020, wata ƙwaƙƙwarar majiya ta tabbatar wa da mujallar Fim.

Ba tun yanzu ba ake ta magana dangane da auren jarumar, amma sai maganar ta yi ƙarfi sai kuma a ji ta yi sanyi. Idan aka tambaye ta sai ta ce ba haka abin ya ke ba, ta na jiran lokacin auren nata dai.

A ‘yan kwanakin nan kuma sai maganar auren ta ƙara tasowa, ya yaɗu a cikin masana’antar finafinai ta Kannywood.

Labarin ya ƙara ƙarfi ne ta yadda aka ga na kusa da ita su na ɗora labarin a shafukan su na Instagram.

Duk da yake labarin ya yaɗu a soshiyal midiya, babu wani jarumi ko wani makusancin ta da ya fito ya ƙaryata shi.

Mujallar Fim ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Halima Atete kan wannan maganar a yau, amma hakan ya ci tura; mun yi ta kiran ta a waya ba ta ɗaga ba, baya ga saƙon tes da mu ka tura mata.

Sai dai ɗaya daga cikin makusantan ta, Isah Bawa Doro, ya tabbatar mana da gaskiyar maganar auren, inda ya shaida mana cewar ai an ma ɗaga auren ne, shi ya sa ba a yi ba.

Ya ce, “An shirya za a yi auren ne a cikin wannan watan na Disamba, amma sai aka ɗaga shi zuwa watan Janairu na sabuwar shekara.”

Da mu ka tambaye shi wanene Halima za ta aura, sai ya ce, “Har yanzu babu wanda zai iya faɗa maka mutumin da Halima ɗin za ta aura domin kowa hasashe ya ke yi.

“Amma dai magana mafi ƙarfi, ana zaton za ta auri mawaƙi Isiyaku Ferus, mawaƙin siyasar nan da ya yi tashe wajen waƙar Shugaba Buhari da jam’iyyar APC, domin kuwa shi ne aka fi sanin su na soyayya da jarumar tsawon lokaci, kuma soyayyar tasu ba a ɓoye ta ke ba.

“A tsawon zaman Halima Atete a harkar fim, babu wani da aka taɓa ganin ta bayyana soyayyar sa a fili kamar sa, don haka ne aka fi kyautata zaton shi ne angon na Halima Atete.”

Ko ma dai me ake ciki, ranar za ta zo, kuma za a ga mijin da za ta aura ɗin.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan