Kimanin Ma’aikatan Zamfara 5000 Ba Za Su Samu Albashin Disamba Ba

272

Ma’aikata 4,972 a jihar Zamfara ba za su samu albashisu na watan Disamba ba har sai an tabbatar da ingancinsu a matsayin sahihan ma’aikata, in ji Kwamishinan Kuɗi na Jihar, Alhaji Rabi’u Garba Gusau.

Da yake yi wa manema labarai jawabi a Gusau, babban birnin jihar, Mista Rabi’u ya ce jihar akwai rashin bin ƙa’ida da yawa a jihar, abinda ya tilasta gwamnatin jihar ɗaukar wannan mataki.

Ya ƙara da cewa an gano wannan matsala ne bayan shi da Babban Sakataren Ma’aikatar Kuɗi sun gudanar da binciken ma’aikata.

Ya ce kuɗaɗen da aka gano ma’aikatan bogi suna karɓa sun kai miliyan N216, kuma wasu daga cikin matsalolin da aka gano sun haɗa da yadda wasu ma’aikatan babu bayanansu a Rumbun Tattara Bayani na Babban Bankin Najeriya, CBN, sannan suna amfani da sunan da ba shi ne a bankuna ba.

Sauran matsalolin sun ne karɓar albashi fiye da guda ɗaya, kamar yadda CBN ya gano, asusun bankuna da aka ɗora ba tare da Lambar Tantance Asusun Banki, BVN ba, ɗora mutanen da ba a sani ba a matsayin ma’aikata a kan tsarin albashi ba tare da amincewar gwamnan jihar ba, karɓar albashi bayan ritaya da sauransu.

Mista Garba ya ce duk wani ma’aikaci da yake da sahihin ƙorafi ya kamata ya zo tantancewa, saboda duk wanda aka kama yana cutar mutane za a hukunta shi.

Ya ce za a raba fama-faman sabunta bayanai ga ma’aikata don inganta adana bayanai.

“Bisa wannan abu da yake faruwa, mun shigo da Daraktan Kuɗi Da Lissafi, Daraktan Kuɗi da Kayayyaki, Daraktan Albashi da duk wani jami’i da haƙƙin sauran Ma’aikatu, Sashe-Sashe da Hukumomi, MDAs ke kansu a jihar don kyautata ayyukanmu. Wannan shi ne abinda muka sa a zuciyarmu, kuma ba za mu saurara ba har sai mun fito da abinda yake ɓoye fili.

“Mun gano cire kuɗaɗe ba bisa ka’ida ba da aka yi daga kuɗaɗen da ma’aikatan gwamnati suka sha wahalar samu, kuɗaɗen da Gwamna Muhammad Matawalle ya biya, kuma mun yi maganin irin ɓannar da ake yi wa lalitar gwamnatin jihar”, in ji Mista Garba.

Ya ƙara da cewa: “Wannan ba mugunta ba ce ko kaɗan, amma wani yunƙuri ne da ake yi don a ba jihar Zamfara mafi kyawun abinda ta cancanta; saboda haka, wannan gwamnati ba za ta lamunci duk wani keta doka ba, kuma dole ma’aikatanmu su zama masu jajircewa da nuna ƙwarewa wajen gudanar da ayyukansu”.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan