Saboda Aƙidar Addini Ake Tuhumar El-Zakzaky- Shi’a

184

Ƙungiyar Shi’a ta ce gwamnatin ƙasar nan tana tuhumar jagoranta ne, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky saboda akidarsa ta addini, amma ba don ya aikata laifuka ba.


Ƙungiyar ta bayyana El-Zakzaky a matsayin fursunan imani, tana mai musanta ikirarin Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed da ke cewa, ana tuhumar malamin ne saboda zargin aikata manyan laifuka.

Ministan ya fadi haka ne a yayin mayar da martani akan rahoton da ke bayyana ƙasar nan da Comoros da Rasha da Uzbekistan da Cuba da Nicaragua da Sudan a matsayin ƙasashen da ke keta ‘yancin gudanar da addini.


Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo ya ce, an sanya ƙasar nan a cikin kundin Bin-Diddigi saboda yadda take cin zarafin wasu mutane masu saboda akidarsa ta addini.


Mai magana da yawun Kungiyar Shi’a Ibrahim Musa, ya ce ya dace a dauki mataki akan hukumomin gwamnatin Muhammadu Buhari bisa aika kisan gilla.


Ƙungiyar Shi’a na zargin sojojin ƙasar nan da kashe mata dubban mabiya tare da binne su a katafaren kabarin bai-daya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan