‘Yan Shi’a Sun Halarci Bikin Kirsimeti A Zariya

152

A ranar Laraba ne ‘yan Ƙungiyar Gwagwarmayar Musulunci ta Najeriya, IMN, da aka fi sani da Shi’a suka halarci Bikin Kirsimeti a Majami’ar Church of the Advent dake Samaru, Zariya.

Da yake jawabi a yayin wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, jim kaɗan bayan ta ziyarar, jagoraran tawagar ‘yan Shi’ar, Farfesa Isa Hasaan-Mshelgaru ya ce maƙasudin halartar bikin shi ne a ƙarfafa soyayya, juriya da fahima a tsakanin ‘yan Najeriya.

“Mun zo ne don mu yi bikin Kirsimeti da ‘yan uwa Kiristoci a nan saboda muna ganin su a matsayin ‘yan uwa, kuma ba mu da abinda za mu ba su idan ba mu zo mu yi murna da wannan rana tare da su ba.

“Yadda suke kallon wannan rana da muhimmanci, haka mu ma muke ganin ta da muhimmanci. Mun ga ya dace mu zo mu ziyarce su don a goge wasu abubuwa marasa kyau da aka ƙirƙira.

“Akwai shingaye da yawa da suka katange mu waɗanda ba za a iya gani ba, waɗanda suka nesanta mu da juna, to muna so mu cike wannan gurbin don mu zama ‘yan uwa maza da mata waɗanda za su zauna a ƙasa ɗaya, a gari ɗaya”, in ji shi.

Mista Hassan-Mshelgaru ya yi kira ga sauran ‘yan Najeriya, Musulmi, Kiristoci ko Maguzawa da su yi watsi da dukkan nau’o’in nuna ƙiyayya, yana mai cewa addini ba yana nufin nuna ƙiyayya ba, amma wata hanya ce ta haɗa kan jama’a.

Limamin Majami’ar, Reverend Isuwa Sa’idu ya nuna jin daɗi bisa ziyarar, ya kuma yi kira ga masu ziyarar da su ci gaba wannan abin kirki don ci gaban ƙasar nan.

NAN ya ruwaito cewa masu ziyarar sun bada kyaututtuka ga Majami’ar a matsayin wata alamar soyayya.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan