Home / Labarai / Ɓarawo Ya Saci Kuɗi A Banki Tare Da Watsarwa A Matsayin Kyautar Kirsimeti

Ɓarawo Ya Saci Kuɗi A Banki Tare Da Watsarwa A Matsayin Kyautar Kirsimeti

Wani dan fashi da ya saci kudi daga wani banki a jihar Colorado da ke Amurka ya yi ihu “Merry Kirsimeti” kuma ya warwatsa kudin da ya sata a gaban bankin.


A sanarwar da kafafen yada labarai na gida suka fitar David Wayne Oliver me farin gemu dan shekaru 65 ya saci kudi daga banki kimanin dala dubu 10 wanda ya warwatsa su akan masu wucewa.


An yi ikirarin cewa dan fashin ya yi barazana da bindiga ga ma’aikatan bankin yayin fashin amma ‘yan sanda sun bayyana cewa babu alamar amfani da bindiga a satar.


Shaidun gani da ido sun ce Oliver ya yi ihu “Merry Kirsimeti” a lokacin da ya fita daga bankin yana fitar da kudi daga jaka. Wadanda suka karbi kudin sun mayar wa bankin kudaden.


Bayan faruwar lamarin, Oliver ya zauna a wani kanti kusa da bankin yana jiran ya mika wuya inda ‘yan sanda suka tsare shi.

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *