Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano a matsayin “gogaggen ɗan siyasa”, mai gina jam’iyya, kuma mutumin da koyaushe yake aiki don ganin nasarar jam’iyyarmu”.
Waɗannan kalamai na Shugaba Buhari suna ƙunshe ne cikin saƙon taya murnar zagayowar ranar haihuwa wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa na Musamman Kan Kafafen Watsa Labarai, Garba Shehu ya fitar ranar Laraba a Abuja.
Yayinda yake taya Gwamna Ganduje murnar cikar sa shekara 70, Shugaba Buhari ya ce: “Gwamnan Jihar Kano shi ne ɗaya daga cikin ‘yan siyasa da suka fi kowa haƙuri da lissafi da na taɓa haɗuwa da su a rayuwata.
“Kuma Ganduje jajirtaccen ɗan jam’iyya ne wanda ya yi aiki ba tare da gajiyawa ba don ta yi nasara”.
Shugaban Ƙasar ya bayyana cewa: “Ganduje yana da duk wani dalili na nuna godiya ga Ubangiji bisa cika shekaru 70 cikin kyakkyawar lafiya.
Shugaba Buhari ya kuma taya Gwamna Ganduje murna bisa lashe kyautar Gwamnan Jam’iyyar APC Da Ya Fi Kowa Aiki, kyautar da Ƙungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC ta ba shi.

[…] Muƙalar Da Ta GabataGanduje Gogaggen Ɗan Siyasa Ne- Buhari […]