Ganduje Ya Hana Cakuɗuwar Maza Da Mata A Baburan A Daidaita Sahu

189

Gwamnatin jihar Kano ta hana cakuɗuwar maza da mata a baburan a babura masu ƙafa uku na A Daidaita Sahu a jihar daga shekara ta 2020 mai kamawa, a wani yunƙuri na magance rashin ɗa’a.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar ya bayyana haka ranar Laraba a taron Annual Vacation Course, IVC, da Ƙungiyar Ɗalibai Musulmi ta Ƙasa, MSSN, Reshen Jami’ar Bayero ta Kano, BUK ta shirya.

Gwamnan, wanda ya samu wakilcin Kwamanda Janar na Hukumar Hisba, Harun Ibn-Sina, ya ce dalilin hana cakuɗuwar maza da matan shi ne cusa ɗabi’un Musulunci da kuma tilasta aiki da dokokin Musulunci a jihar.

Gwamna Ganduje ya kuma yi kira ga mahalarta taron da su mayar da hankali a kan karatu, su kuma guje wa shan ƙwaya, abinda ya ce hana lalata rayuwar matasa.

A jawabinsa, Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Abubakar Sa’ad III, ya ƙaryata iƙirarin Amurka cewa ana zaluntar Kiristoci a Najeriya.

Sarkin Musulmin ya ce ya kuma kaɗu matuƙa da maganar da Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN ta yi cewa ana zaluntar su a Najeriya.

Ya ce da da akwai zaluncin da suke magana, da tuni batun ya je gaban Majalisar Tattaunawa Tsakanin Addinai, Interfaith Forum, inda shugabannin Musulunci da na Kiristanci ke haɗuwa lokaci-lokaci don tattauna batutuwan da za su inganta zaman lumana a tsakanin addinan.

Sarkin Musulmin ya lura da cewa mafi yawan laifukan da makiyaya Fulani ke aikatawa ba suna yin sa ba ne ta fuskar addini, saboda ba duka Fulani ba ne Musulmai.

A cewarsa, Fulani da yawa ba su da addini, abinda ya dame su kawai shi ne su kare shanunsu.

Sarkin na Musulmi ya yi kira ga al’ummar Musulmi da kada su bari waɗannan kalamai su fusata su, kalaman da ya bayyana a matsayin na ƙarya kuma na son kai.

A nasa jawabin, Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya gargaɗi Musulmi game da tara buƙatu da suka fi ƙarfin su.

Sakin ya danganta ƙaruwar yara da ba sa zuwa makaranta a Arewa da yadda ake auren mata fiye da ɗaya ya yi yawa da kuma yawan sake-sake.

Ya nuna rashin jin daɗi bisa yadda yankin Arewa Maso Gabas mai cike da Musulmi da kuma sassan Arewacin Najeriya suka zama yankuna mafiya talauci saboda rashin fahimar Musulunci.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan