Kwantan Wasa Tsakanin Nasarawa Da Kano Pillars

190

Ayau Alhamis za a fafata kwantan wasa tsakanin kungiyoyin kwallon kafa guda biyu da suke daga arewacin Najeriya.

Inda za a fafata wasan tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa United da Kano Pillars acan babban birnin jahar ta Nasarawa wato Lafia wasan da aka yiwa lakabi da Boxing Day.

Ita dai Nasarawa United babu ‘yan kallo take buga wasannin ta na gida ahalin yanzu biyo bayan rashin da’a da magoya bayanta sukayi a wasansu da kungiyar kwallon kafa ta Plateau United inda har aka cisu tara.

Kano Pillars dai ayanzu haka suna matsayi na 11 da maki 13 inda ita kuma Nasarawa United tana matsayi na 20 inda take da maki 5.

Amakon daya gabata kowacce kungiya acikinsu tasami nasarar lashe wasanta, inda Nasarawa United ta sami nasarar farko akan Heartland daci 2 da 1 tun bayan da aka fara gasar, ita kuwa Kano Pillars tasha dakyar ahannun Ifeanyi Uba daci 1 mai ban haushi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan