Mambobin ASUU Sun Samu Albashin Disamba Duk Da Bijire Wa Tsarin IPPIS

244

Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi ya ce malaman jami’o’i sun samu albashin Disamba duk da ƙin shiga Dunƙulallen Tsarin Biyan Albashi, wato IPPIS.

Gwamnatin Tarayya, ta bakin ofishin Akanta Janar na Ƙasa, ta yi barazanar cewa duk wani malami da bai shiga tsarin IPPIS ba ba za a biya shi albashin Disamba ba.

To amma, shugaban na ASUU ya ce binciken da suka gudanar a jami’o’in gwamnati ya nuna cewa malaman sun samu albashin Disamba duk da cewa sun ƙi shiga tsarin na IPPIS.

Mista Biodun ya bayyana haka ne a saƙon da ya tura wa mambobin ASUU don taya su murnar bikin Kirsimeti.

Shugaba na ASUU ya yi kira ga mambobin ƙungiyar da su shirya fuskantar ƙalubale a sabuwar shekara.

Ya ce ‘yan Najeriya suna shan wahalar rayuwa ne saboda tsauraran manufofin tattalin arziƙi na gwamnati ma ci, yana mai ƙarawa da cewa yanayin ya sa rayuwa ta yi wa talakawa tsauri, yayinda masu ɗan abin hannu kuma suke ci gaba da azurta kansu ba tare da kula da marasa galihu ba.

Ya ce talakawa da marasa galihu ba su da abinda za su yi bikin Kirsimeti da shi.

A cewar Mista Ogunyemi, taɓarɓarewar tattalin arziƙ ta kai talakawa maƙura, kuma ta mayar da bukukuwan ƙarshen shekara ba su da wata ma’ana.

Ya ce bukukuwan sin fi ma’ana idan gama-garin ‘yan Najeriya suna da damar samun ilimi mai nagarta, lafiya da sauran kyawawan abubuwan rayuwa.

Ya ƙara da cewa akwai alamomi cewa ɓangaren ilimi mai zurfi zai zafafa shekara mai kamawa biyo bayan ƙin shiga tsarin IPPIS da mambobin ASUU suka yi.

“‘Ya ‘yan ƙungiya, yayinda muke bin sahun sauran sassan duniya don shiga hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara, mu yi duba da godiya da kuma shirya fuskantar ƙalubalen gaba. Wannan lokaci na nuna soyayya yana tunatar da mu nauyin da yake kanmu na kula da talakawa da gajiyayyu.

“Biki irin wannan ya fi ma’ana idan gama-garin ‘yan Najeriya suna da damar samun ilimi mai nagarta, lafiya da sauran kyawawan abubuwan rayuwa. Ina taya ku murnar hutu yayinda gwagwarmaya za ta ci gaba, Biodun Ogunyemi”, in ji shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan