Waye Zai Yi Kuka Idan Sarki Sanusi II Ya Tafi? – Farfesa Umar Labdo

  1589

  A ‘yan kwanakin nan ana ta cecekuce dangane da rikicin da ya taso tsakanin Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi.

  A yayin da wasu ke ganin wannan rikici babban cikas ne ga ci gaban jihar Kano da hadin kanta, wasu na duban lamarin a matsayin rikicin siyasa tsakanin shugabanni biyu wadanda, kamar yawancin jagororin Arewacin kasar nan, ba maslahar al’umma ce ko ci gaban kasa ya dame su ba. Abinda yake gabansu shi ne maslahohinsu na kashin kansu da kosar da kibriya’insu.

  A ganin yawancin talakawan jihar Kano, da ma talakawan Arewacin Nijeriya, Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi dan juma ne da dan jummai. Shugabanni ne masu ananiyya, wadanda tarihin rayuwarsu da maganganunsu da aikace-aikacensu ke nuna ina suka karkata.

  Wasu masharhanta da suka yi fashin baki a kan lamarin suna ganin cewa, Gwamna Ganduje yana amfani da iko da yake da shi a matsayinsa na gwamna mai wukar yanka (executive governor) don ya tursasa Sarkin Kano Sanusi, ya nuna masa iyakarsa. Wannan kuma, a ganinsu, cin fuska ne ga daukacin ‘ya’yan masarautar Kano kuma kokarin rusa tarihi ne da wargaza hadin kan masarautar.

  Wasu kuma suna ganin cewa, ai shi ma Sarki Sanusi, a tsawon shekaru biyar da ya share yana kan karagar mulki, babu abinda ya yi sai kokarin rusa tarihin masarautar da warware duk wata tufka da magabata wadanda suka kafa masarautar suka yi. Masu wannan mahanga suna nuni da irin ra’ayoyi da manufofin da Sarkin ya yi ta kira zuwa gare su kuma ya yi ta kokarin dabbaqa su da tabbatar da su.

  Maganganun Sarkin Kano Sanusi da rubuce-rubucensa da ayyukansa, tun shekaru da yawa kafin ya zama sarki har zuwa yau, ba sa nuna shi a matsayin wanda ya yi amanna da tarihin al’ummarsa da al’adunsu ko shika-shikai da durakun masarautar da ya gada. Ra’ayoyin Sarkin Kano Sanusi suna nuna shi a matsayin dan Boko mai ra’ayin gaba-dai-gaba-dai, wanda yake da nufin sauya tsarin rayuwar Kanawa, ya yi waje da kayan gadonsu na addini da al’ada, da duk wani abinda suke dauka da kima ko daraja.

  Manufofin Sarki Sanusi dangane da tsarin rayuwar iyali na Musulmi yunkurin tabbatar da ajandar Turawa ne ta sabule rayuwar Musulmi daga Shari’ar Musulunci da mayar da su kan tafarkin Nasara.

  Kira da Sarki Sanusi ya yi ga matar aure Musulma cewa idan mijinta ya mare ta ta rama, yaki da yake yi da auren wuri, yaki da yake yi da auren mace fiye da daya, aike diyarsa da ya yi zuwa Abuja don ta tsaya tsirara a bainar jama’a (ba rufin kai ba lullubi, wuyanta a waje, kunnenta da ‘yan kunnenta a waje, tsintsiyar hannunta a waje) duka wannan yaki ne da addinin Kanawa da al’adunsu, da abinda iyayen Sanusi da kakanninsa suka zub da jini, suka yarfe gumi, don tabbatarwa.

  Dangne da kawo ci gaba da inganta rayuwar Kanawa, me Sarkin Kano Sanusi ya kulla a shekaru biyar da ya yi bisa karagar sarautar Kano? Ina makarantar da ya gina, ina masana’antar da ya kafa, ina jarin da ya janyo daga abokan huldarsa na gida da na waje don habaka tattalin arzikin Kano? Ina kokarin da Sarkin Kano Sanusi ya yi don rage ta’ammali da kayan maye a tsakanin matasa da matan Kano?

  Kudade da Sarki Sanusi ya kashe wajen gyaran fadarsa, da sayen zunduma-zunduman motoci masu numfashi da masu minshari da masu kakari, da sayen kayan ado da kawa da kwalliya har wasu suka yi masa lakabi da Sarki Dawisu, irin wadan nan malkudan kudade da ya kashe rabinsu wajen inganta rayuwar Kanawa babu shakka da yanzu an gani a kasa.

  Irin wadan nan abubuwa ne suka sa wasu ke ganin cewa Sarki Sanusi dai sana’ar Turawa ne, watau Turawa ne suka kafa shi, suka jingina masa tsani ya hau, suka ciccida shi ya kure a sana’arsa ta banki, ya kai koli a gadon gidansu, duka don ya yi musu hidima. Kuma hidimar dai annan shina yi.

  Don haka idan an ragewa Sarki iko, ta hanyar fasa masarautar Kano zuwa gida biyar, ko ma daga karshe an tsige sarkin dungurum, wane ne ya yi rashi: Kanawa ko Turawa? Waye zai yi kuka idan Sarki ya tafi?

  Da yawa na ganin idan Sarki ya tafi ba Kanawa ne za su yi kuka ba, wasu ne dabam za su yi. Wadanda za su yi kuka su ne Turawa wadanda yake wa manufofin su hidima, wadanda suke ba shi lambobin girma iri-iri, suna zuga shi, suna sannafa shi cikin mutane dari masu karfin fada-a-ji a duniya.

  Wadanda za su yi kuka su ne almajiran Turawa na cikin gida masu manufofi da ra’ayoyi irin nasa, wadanda suke kallon sa a matsayin gwarzon “turantar” da Hausawa da sauya rayuwar Malam Bahaushe zuwa tsarin Nasara.

  Wadanda za su yi kuka su ne ‘yan uwansa ‘yan duniya, hamshakan attajirai da matasan ‘yan siyasa, wadanda duk sanda ya ballo ruwa suke toshewa ta hanyar sayen ‘yan majalisa ko tattaro dattawan Arewa don su yi sulhu.

  A karshe, wannan maqala ba goyon bayan Gwamna Ganduje ba ne a cikin rikicinsa da Sarki Sanusi. Manufar maqalar ita ce bayyanawa duniya matsayin da yawa daga cikin talakawan Kano, da ma Arewa baki daya, dangane da wannan badakala wacce wasu za su so a ce da sunan talaka ake yi, ko don kare maslahohinsa.

  A wajen talakan Kano wayayye fadakakke, Ganduje da Sanusi dan juma ne da dan jummai. Duka shugabanni ne masu rawa da bazar talaka, amma ba su damu ba idan ya fada kwata.

  Farfesa Umar Labdo Malami Ne A Jami’ar Yusuf Maitama Sule Da Ke Kano

  Turawa Abokai

  1 Sako

  1. Wannan maganar tsagwaron qarya ce domin inda Mai Martaba Sarki Sunusi aikin turawa yake da wallahi ko Buhari bai iya taka shi ba, bare wani gwamna ko a satin nan turawa sun sa baki ansaki masu badaqalar da hankali bazai yarda ba, sannan kowa ya sani cewa duk wani Abu yana da amfani da rashin amfani amma kace baka goyon gwamna amma Ka nemo yadda zaka kushe Sarki baka fadi alherin Shi ko daya ba, sannan kuma baka kushe gwamna ko sau daya ba, da wannan zamu iya gane boyeyyar manufar Ka ta kasami cigaba a Jami’a domin munsan jami’ar Ku tana qarqashin gwamna ne. Allah ka raba Mu da biyewa son zuciya. Ameen Ameen

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan