Tsarin Iyali Ne Hanyar Shawo Kan Matsalar Almajiranci A Arewa – Sarki Kano Sanusi II

213

Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga al’ummar yankin arrwacin ƙasar nan da su rage yawan ‘ya’yan da za su haifa saboda samun damar kula dasu, kuma su auri adadin yawan matan da za su iya adalci a zamantakewarsu.

Sarki Sanusi II ya bada wannan shawarar ne a bikin taron ƙungiyar musulmai ta ƙasa karo na 108 wanda ƙungiyar ta shirya a sansanin ta na dindindin da ke kan babban titin Legas zuwa Ibadan a jihar Ogun.

Sarkin ya jaddada cewa matsalar almajiranci da ake samu a ƙaar nan ba matsalar addini bace, da kanmu zamu iya shawo kanta domin tana ci wa al’ummar arewacin ƙasar nan tuwo a ƙwarya.

Tun da farko da Sarkin ya bayyana ƙalubalen almajiranci, waɗanda su ka haɗa da: “ƙananan yara da ba sa zuwa makaranta wadanda iyaye ke mika wa malamai, amma kuma su bige da bara a titunan faɗin ƙasar nan”

“Akwai miliyoyin ƙananan yara da ke almajiranci a faɗin ƙasar nan duk da ƙoƙarin gwamnati domin shawo kan wannan matsalar”

Ya ƙara da cewa akwai bukatar a mayar da yaran makaranta, hakazalika Sarki Sanusi ya ce akwai bukatar iyaye maza su dinga auren yawan matan da zasu iya rikewa.

“Idan muka cigaba a haka, akwai yuwuwar kashi 40 na mutane da zamu haifa a Najeriya zasu fada tsananin talauci. Talauci a Kudu maso yamma ya kai kashi 20, a Arewa kuwa kashi 80 ne, Legas na da kashi 8 amma jihar Zamfara kashi 91 ne.”

“Munata kokarin shawo kan matsalar almajiranci, a kan me mutane za su haifi ‘ya’yan da ba zasu iya kula dasu ba?


Adalci garesu da kanka shi ne idan zaka iya kula dasu. A maimakon haihuwar ‘ya’ya da yawa, me zai sa ba zamu haifa yawan wadanda zamu iya kula dasu ba?

Da yawa daga cikin yaran kan koma bangar siyasa ko yawo a titi saboda rashin kula.”


“Wannan ce shawarata a kan yawan tara yara. Ba matsalar addini bace, matsala ce a tsakaninmu wacce zamu iya shawo kanta da kanmu.” in ji Sarki Sanusi II

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan