Jami’ar Bayero ta Kano, BUK, ta bada tallafin karatu ga ɗalibai 300 marasa galihu ‘yan asalin jihar Kano don su yi amfani da shi a shekarar karatu ta 2019/2020 mai kamawa.
Shugaban Jami’ar, Farfesa Muhammad Yahuza Bello, ya bayyana haka yayinda yake karɓar baƙuncin wakilan Ƙungiyar Tsaffin Ɗaliban Jami’ar Aji na ’92’ ranar Juma’a a Ofishin Majalisar Dattijan Jami’ar.
Mista Bello, wanda ya bayyana jin daɗi ga mambobin ƙungiyar bisa bada naira miliyan N1 a matsayin tallafin karatu ga ɗalibai ‘yan asalin Kano, ya bayyana ‘Yan Aji na ’92’ a matsayin ɗaya daga cikin ƙungiyoyin tsaffin ɗalibai mafiya motsi a jami’ar.
Shugaban Jami’ar ya kuma yabi yadda ƙungiyar ke yin ayyukan jin ƙai a rayuwar ɗan Adam, musamman tallafa wa ɗalibai, wanda ya ce ya zo a lokacin da ya dace, saboda ana dab da fara rijistar ta shekarar karatu ta 2019/2020.
Da yake jawabi tunda farko, Shugaban Ƙungiyar Ɗaliban ta Jami’ar Bayero Aji na 92, Reshen Jihar Kano, Alhaji Ɗahiru Muhammad Sa’id, ya ce ƙungiyar ta bada fifiko ne ga ci gaban ilimi ta hanyar haɗa kai da shugabancin jami’ar da sauran masu ruwa da tsaki.
“Manufar wannan ƙungiya ta farko ita ce ƙirƙirar wani tabbataccen tsari wanda zai amfani mambobinta da al’umma gaba ɗaya”, ya bayyana haka.
A ta bakinsa, ƙungiyar ta yi nasarar biyan kuɗaɗen tara na mazauna gidajen yari da kuma diyya a Babban Gidan Yari na Kano; biyan kuɗaɗen magani ga marasa galihu a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, AKTH da kuma tallafin kuɗi ga iyalan abokan aiki da suka rasu.