Ina Neman Matar Aure – Janaral Babangida

259

Tsohon shugaban ƙasar nan a mulkin soji Janaral Ibrahim Badamasi Badamasi Babangida mai ritaya, ya bayyana cewa ya fara neman matar aure.

27 Feb 1990, Paris, France — Nigerian President Ibrahim Babangida arrives in Paris for a four-day official visit to France. — Image by © Reuters/CORBIS

Janaral Babangida ya fara da bayyana irin kalar matar da yake so ya aura, ya bayyana cewa duba da irin shekarunsa, yana neman mai tarin shekaru wacce bazata samu matsala domin ta aureshi ba, haka zalika itama bazata takura ba.

Tsohon shugaban ƙasar mai shekaru 78, ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke wata ganawa da jaridar SUN, inda ya bayyana tsoron cewa bazai samu wacce za su yi irin zaman da sukayi da marigayiyar matarshi, Maryam ba.

“Eh lallai da gaske na ke. Ina dubawa kuma ina da yakini. Sai dai abin lokaci yana kurewa. Lokaci na cigaba da tafiya, lamarin yana sake shiga matsala.”


“Idan ya kara tsayi, zan tsufa sosai, kuma tunanin samun wata matar auren zai gushe. Amma zan yi kokari in samu kafin lokacin ya zo.”


“Idan akwai wata a kusa, za’a iya hada wa a cikin watanni 3 ko 6. Saboda dole dama sai daga cikin wadanda ka dade da sani ko kuma cikin makusantanka, tinda bazai yiwu kace kawai kana neman aure ba.”


“Duk da haka, zan yi adalci wajen neman matar. Ina matukar son yi adalci. Misali, Ba zan nemi yarinya karama wacce na kere mata ba saboda hakan zai zame mana matsala gaba daya.”

“Dole in yi adalci. Abu na biyu shine, Ina tunanin da wacce zan samu ko zamu iya irin zama irin wanda mukayi da Maryam, wanda hakan a yanzu yana da wahala. Ina dai cigaba da addu’a kuma ina tunanin hakan zata kasance.”

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan