Hakika Kunya na da matukar muhimmanci wajen kowanne mutum musamman a wajen Mace kasancewar ta jigo wajen bayar da tarbiyya, sau tari akan danganta ita kunyar gaba ɗayanta da siffofin mata, hakan tasa wasu lokutan idan Namiji ya cika kunya sai kaji ana “sai kace Mace”?
Haka kuma kunya na ɗaga daraja da kimar mutum, tana kuma sa a kasance mai tarbiyya da biyayya da da’a da kuma kamala.
To, tunda hakane yana da kyau ƙwarai ko wace mace ta siffatu da wannan ɗabi’a mai Kyau da muhimmanci kasancewar ita kunya na taimakawa wajen tabbatar da tarbiyya da nutsuwar mutum musamman ita mace.
Tabbas ko ba’a fada ba kunya na karawa mace kyau ta kuma sai mata mutunci a idon mutane (na tabbata babu wanda zai so ace ƴarsa ko matar sa ko ƙanwarsa ta kasance marar kunya) sannan ta kan zamo kariya a gareta (mace), abin nufi da kariya anan shi ne; duk macen da take da kunya to zaka samu maganar ta akwai tsabta a cikinta, (koda kuwa a rubuce ne) zaka same ta da tsare mutunci da Kuma gudun aikata abinda za’ayi Allah wadai da ita, sannan takan yi kokari wajen kin kula wanda zai kawo mata matsala a cikin al’amuran ta, zaka sameta da nutsuwa da bin al’amura sannu sannu da kuma kawaici wanda kusan duk mai kunya ba’a rabashi da shi.
Duk wani abu in aka hadashi da kunya to takan karawa abin inganci da kyau, hakkan tasa ko wajen neman aure mace in ta kasance mai kunya sai ta kara martaba da ƙima a idon mai neman auren, abokai da danginsa.
Amma rashin kunya a wajen Mace nada illa kwarai, domin takan haifar mata da matsaloli masu tarin yawa, domin kunya wata alamace dake nuna cewa mace nada kyakkyawar tarbiyya inda rashin ta ke nuna cewa akwai karancin tarbiyya a tare da ita.
To ko yaya matsayin kunya yake a yanzu Musamman a bangaren Mata?
Hakikanin Gaskiya ko ba’a fada ba abune da yake a bayyane a halin yanzu akwai ƙarancin Kunya a tsakanin mutane musamman matasa baga mazan ba baga matan ba wanda su aka fi so su suffatu da wannan dabi’a.
Kaɗan daga cikin matsalolin da watsi da dabi’ar kunya kan haifar:
Rashin Biyayya: Muddin aka samu mutum da karancin kunya koma ya rasa ta gaba daya to zaiyi wahala yayi biyayya yadda ya kamata wajen na gaba dashi, kusan wannan kalubale ne daya addabi jama’a rashin ganin girman na gaba gare ka.
Lalacewar Tarbiyya: Ƙarancin kunya ko rashinta kan taka muhimmiyar rawa wajen Lalacewar Tarbiyya musamman awajen mace, Mata kusan sun matan cewa kunya wata sifface da ake son ko wacce mace ta kasance tana da ita, yanzu kusan a iya cewa anyi watsi ko an ajiye kunyar a gefe guda da sunan wayewa.
Ba’a ce kar mace ta waye ba, waye wa nada nasa hurumin da amfanin domin shi ita rashin wayewar zaisa ka zamo ko ki zama gidahuma. Amma me? Kibi wayewar ta hanyar da bazata gurɓatarmiki da rayuwa ko kawar miki da wasu halaye da ɗabi’unki masu kyau da daraja ba. Yi koƙari ki tsinci abubuwa masu Kyau da wayewar tazo dashi ki inganta rayuwar ki, kar ki bari wayewar ta bi dake a duk yadda take so ko Kuma duk yadda tazo.
Rashin kunya a wurin mace illa ce babba domin ita kadai tana iya zame mata babbar matsala a rayuwa. Kunya ce ke sa mace ta tsaya matsayinta na mace tare da kyakkyawar tarbiyya. A da idan aka ga mace tana yawan mu’amala da maza, akan yi mata waka cewa Mai wasa da maza karya
Yana da kyau mugane muhimmanci kunya mu Kuma guji aikata abubuwa na rashin kunya, ita kunya kamar sinadari ce domin babu wani abu da za’a hadashi da ita yaki armashi.


Ko laifi mutum ke aikatawa yake kuma kunyar bayyanashi to ana kyautata masa zaton daina wannan laifin saboda yana kunyar bayyanashi fiye da wanda baya kunyar bayyana wani abu mara Kyau da yake.
Wannan shi zai tabbatar mana da cewa Kunya muhimmin al’amari ce duba da yadda takan bawa mutum Kima tare da daga darajarsa cikin mutane.
Jidda Gaya Yar Jarida Ce Mai Zaman Kanta Ta Rubuto Daga Kano