Baitulmalin Ƙasar Nan Na Barazanar Ƙarewa – Obasanjo

138

Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, yayi gargadin cewa kasar nan na fuskantar barazanar karewar baitulmalinta, sakamakon karuwar adadin bashin da gwamnati ke karba.

Obasanjo yayi gargadin ne yayin halartar wani taron addini a birnin Legas, inda ya koka kan yadda ƙasar nan da kuma wasu kasashen Afrika ke ciwo bashi daga bankin duniya, asasun IMF da sauran hukumomi, matakin da tsohon shugaban ya ce idan ba’a yi taka tsantsan ba, zai tagayyara tattalin arzikinsu.

Obasanjo ya kuma ja hankali kan kididdigar da ta nuna cewar, zuwa karshen watan Maris da ya gabata na 2019, adadin bashin da ake bin ƙasar nan a ketare ya kai dala biliyan 81 da miliyan 274.

Sai dai a nata gefen, gwamnatin tarayyaa, ta sha kare kanta da cewar, tana karbo bashin ne, domin cike gibin bukatun gudanar da ayyukan raya kasa da suka hada da noma da kuma samar da ababen more rayuwa, da zummar cimma burin daina dogaro kan arzikin man fetur wajen samun kudaden shiga.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan