Kalaman Sarkin Kano Sanusi II Masu Tayar Da Ƙura

  294

  A cikin kusan shekara 30, Sanusi Lamido Sanusi (Muhammadu Sanusi II daga baya) ya sha shiga cikin kwaramniya da gwamnatoci da ‘yan siyasa da malaman addinin Musulunci.
  A wasu lokutan ma ana ganin wasu matakan da yake dauka suna yin hannun riga da gidan sarauta inda ya fito.

  Malam Muhammadu Sanusi ya taso a cikin gidan sarauta tare da sauran ‘ya’yan sarki, sai dai hakan bai hana shi zama mai ra’ayin kansa ba, kuma ba ya shakkar bayyana ra’ayin.
  Sai dai sau da dama, rashin shiru da bakinsa kan janyo masa mummunan martani daga bangarori daban-daban, musamman wadanda abin ya shafa.
  Wasu na bayyana Sarki Sanusi a matsayin mutum mai karfin zuciya da ba ya tsoron fadar gaskiya komai dacinta a kan ko wane ne kuwa.
  Sarki Sanusi mutum ne da ba ya shakkar bayyana ra’ayinsa ko abin da ya fahimta a fili ba tare da boye-boye ba, ko da kuwa hakan zai janyo masa martani maras dadi.
  Yana cikin mutanen da ake cewa “gaskiyarsu na ja musu tsangwama.”
  Ko a lokacin da aka zabe shi a matsayin sarkin Kano, mutane da dama sun yi mamaki, ganin yadda ya saba janyo ce-ce ku-ce a harkoki daban-daban, sabanin yadda ake ganin al’adar mafi yawan sarakuna da ba kasafai ake jin suna magana kan kowane batu ba.
  Yaushe ya fara tarar aradu da ka?
  Bayan kammala karatu ya fara aikin banki, kuma a iya cewa ya fara da kafar dama, domin ya samu aikin da yake daukar albashi mai tsoka.
  Sai dai a shekarun 1990 an zarge shi da mara baya ga kungiyar ‘yan gwagwarmaya ta Jama’atu Tajdidil Islam (JTI), bayan kungiyar ta balle daga kungiyar ‘yan uwa musulmi Muslim Brothers karkashin Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.
  Lamarin ya kai ga hukumomin mulkin soja na lokacin sun kama shi tare da tsare shi a Sokoto.
  Zargin da aka yi masa na mara baya ga kungiyar ya sa mutane da dama na mamakin alakarsa da ita, ganin cewa yana cikin ‘ya’yan sarauta.
  Makusantansa dai sun musanta cewa ya taba shiga kungiya Muslim Brothers ko JTI . Sun ce an alakanta shi da kungiyar ne domin a bata masa suna a kuma shafa masa kashin kaji.
  Sukar gwamnatin Kano 1999-2013
  A fili take cewa Sarkin Muhammadu Sanusi II bai boye ra’ayoyinsa ba kan salon gwamantin jihar Kano tun daga 1999 zuwa 2013.
  A watan Agusta, 2011 ya yi wani rubutu a jaridu inda ya soki gwamnatin Kano bisa kashe Naira miliyan 719 wajen gina masaukin gwamnatin Kano a Abuja.
  Sabanin ya kai ga gwamnatin jihar a lokacin ta nemi a kori Sanusi Lamido Sanusi (Muhammadu Sanusi II daga baya) daga bankin, to sai dai bankin ya ki aiki da bukatar gwamnatin.
  Ce-ce-ku-ce kan Shari’ar Musulunci
  Bayan komawar Najeriya tsarin mulkin dimokradiyya a 1999, wasu jihohon arewacin kasar sun kaddamar da shari’ar musulunci.
  Kaddamar da shari’ar dai ya zama tamkar yayi tsakanin jihohin bayan gwamnatin Zamfara ta zama ta farko da ta aiwatar da ita.
  Batun shari’a a lokacin ya zama daya tilo da ya dauki hankulan jama’ar arewacin kasar. Babu abin da suke so sama da fara aiki da shari’ar Musulunci.
  Malaman addinin Musulunci sun zama na gaba-gaba wajen matsa wa gwamnatoci lamba don ganin an kaddamar da shari’ar a jihohi.
  To sai dai Sanusi Lamido Sanusi (a lokacin) bai yi shakkar fitowa fili ya kalubalanci kaddamar da shari’ar ba.
  Yana da ra’ayin cewa akwai wasu matsaloli da ke addabar al’umma wadanda su ya kamata a fara magancewa tukunna.
  Wannan ra’ayi nasa ya janyo masa bakin jini a wajen wasu malamai da ke gaba-gaba a fafatukar kaddamar da shari’ar Musuluncin.
  Cikin malaman da suka samu sabanin fahimta har da Marigayi Shaikh Ja’afar Mahmud Adam.
  Gyara a harkokin bankuna a Najeriya
  Kwarewarsa a aikin banki da tattalin arziki ta sa gwamnatin Marigayi Umaru Musa ‘Yar Adua ta nada shi gwamnan babban bankin kasar.
  Cikin matakan farko da ya fara dauka bayan zama gwamnan bankin shi ne, sauke shugabannin wasu manyan bankuna da ke shirin durkushewa, da nada wasu don maye gurbinsu.
  Matakin ya janyo masa bakin jini daga makusantan shugabannin da aka sauke, wadanda a lokacin an yi amanna cewa shafaffu ne da mai.
  To sai dai matakin ya yanyo masa farin jini wajen mafi yawan ‘yan kasa da masana tattalin arziki na duniya.
  Zargin gwamnatin Jonathan da batar da Biliyoyin Naira
  Bisa al’ada, duk wani jami’in gwamnati ba ya fitowa ya soki gwamnatin a zahiri, ko kuma ya nuna cewa wasu abubuwan da ake yi a gwamnatin ba daidai ba ne.
  Amma a karfin hali irin na Sanusi Lamido Sanusi ya sa shi aika wa shugaban Najeriya Goodluck Jonathan wata wasika wadda a ciki ya yi zargin cewa, kamfanin man fetur na kasar NNPC ya karkatar da kimanin dala miliyan 50, cikin wata 18.
  Daga baya ya shaida wa majalisar dattijai cewa
  kimanin dala biliyan 20 ne NNPC bai saka a asusun gwamnti ba.
  A lokacin ya yi gargadin cewa, matukar ba a dauki mataki ba, to tattalin arzikin Najeriya zai iya durkushewa.
  Kamfanin man na Najeriya ya musanta zargin.
  Lamarin ya janyo tayar da jijiyar wuya da sukar gwamnati da kiraye-kirayen gudanar da bincike. Majalisar dattijan kasar ta kaddamar da bincike kan zargin rashin sanya kudin a asusun gwamnati.
  A ranar 20 ga watan Fabrairun 2014, gwamnatin Shugaba Goodluck ta sauke Sanusi daga matsayin gwamnan babban bankin Najeriya a lokacin yana halartar wani taro a Jamhuriyyar Nijar.
  Sai dai wasu bayanai sun nuna cewa tun a watan Disamban 2013 shugaban Najeriya na lokacin Jonathan, ya nemi Sanusi ya yi murabus daga matsayin gwamnan babban bankin Najeriya, amma ya yi kememe.
  Kuma ma Sanunsin ya kalubalacin sauke shi da aka yi , inda ya ce a doka shugaban kasa ba zai iya sauke shi ba, sai dai majalisar dattijai.
  Ya samu nasara a kotu daga baya, inda ya ce da ma babban burinsa ke nan.
  Sabani da Kwankwaso kan almajirai
  A ranar takwas ga watan Yuni aka nada shi sarkin Kano bayan mutuwar Sarki Ado Bayero. Nadin da aka yi masa, ya janyo mummunan martani da zanga-zanga daga masu son a nada jinin Ado Bayero a matsayin Sarkin.
  Sai dai tafiya ba ta yi nisa ba aka fara jin kansu da gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso musamman kan batun hana bara a jihar, da yadda almajirai mata ke taruwa a gidansa yana ba su sadakar abinci.
  Matakin bai yi wa gwamnati dadi ba, don har an aika masa daga gidan gwamnati cewa ya daina tara almanjirai a gidan sarki yana ba su sadaka.
  Sai dai ya mayar wa gwamnati martani cewa da kudinsa yake bayar da sadakar ba da kudin gwamnati ba.
  Sai dai tafiya ba ta yi nisa ba, aka yi zabe Kwankwaso ya bar mulki, mataimakinsa Abdullahi Umar Ganduje ya gaje shi.
  Sukar Boko Haram
  A watan Nuwamban 2014, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi magana kan Boko Haram, inda ya ce ya kamata jama’a su kare kansu daga hare-haren kungiyar.
  Sarkin ya yi wannan kira ne a lokacin da ake tsoron fitowa fili a soki Boko Haram, saboda yadda suke kai hare-hare ba kakkautawa.
  A watan Disamba shugaban kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar da wani bidiyo inda ya yi barazanar kai wa Sarkin na Kano hari da kuma hallaka shi.
  Sai dai duk da barazanar, Sarkin na Kano bai nuna wata fargaba ko tsoro ba, maimakon haka ma ya kara mayar wa Shekau martani, inda ya ce, Allah yana ba shi kariya. Kuma babu abin da Shekau zai iya yi masa.
  Dokar auratayya
  A watan Fabrairun 2017 Sarki Sanusi ya bijiro da wani yunkuri na sauya zamantakewar al’umma, musamman ma batun aure da tarbiyyar yara .
  A karkashin kudurin dokar, sarkin ya so a hukunta duk namijin da ya doki matarsa, haka kuma a yanka wa mijin da ya saki matarsa wani kudi da zai ba ta domin ci gaba da rayuwa, sannan a tilasta masa daukar nauyin ‘ya’yansa ciki har da karatunsu.
  Haka kuma kudurin dokar ya yi tanadin cewa a hana aurar da kananan yara da ba su kai shekarun aure ba.
  Lamarin ya janyo wa Sarkin Kano mummunar suka daga malaman addinin Musulunci , inda suka zarge shi da yunkurin kawo sabon abu a addinin.
  Wasu ma har sun yi zargin cewa wata kwangila ce sarkin da wasu mutane suka karbo daga Turawan Yamma don gurbata tsarin addinin Musulunci.
  Sai dai Sarkin ya musanta wannan zargi.
  Kuma ya tsaya kai da fata cewa ya fito da tsare-tsaren ne don masalahar al’umma, musamman ma duba da irin korafe-korafen da yake karba kallum a fadarsa dangane da auratayya da zamantakewa.
  Sarki Sanusi da Gwamna Yari
  A watan Afrilun 2017 gwamnan jihar Zamfara na lokacin Abdulaziz Yari ya bayyana cewa sabon Allah ne ya janyo annobar ciwon sankarau da jihar ke fama da ita.
  Kalaman nasa sun janyo martani daga al’umma. To sai dai babu wani shugaba da ya fito fili ya kalubalanci kalaman sai sarkin Kano Muhammadu Sanusi wanda ya saba tarar aradu da ka.
  Yayin da yake jawabi a wurin wani taro kan harkokin zuba jari a Kaduna, Sarki Sanusi ya ce bai kamata mutum mai mukami irin na gwamna ya rika alakanta abin da ya shafi kiwon lafiya da sabon Allah ba.
  A cewarsa, “Mutum sama da 200 sun mutu, an tambayi gwamna amma ya ce wai sabon Allah ne ya sanya hakan. Bai kamata a rika yin irin wannan jawabi ba. Wannan kalami da {Yari} ya yi bai yi daidai da koyarwar Musulunci ba.”
  “Idan ba shi da maganin riga-kafin sankarau, sai kawai ya je ya nemo”, in ji mai martaba Sarkin na Kano.
  Sai dai shi ma gwamnan na Zamfara Abdulaziz Yari ya mayar wa sarkin Martani inda ya ce tabbas sabon Allah ne ya kawo annobar.
  Ya kara da cewa zai iya kawo wa sarkin ayoyin Kur’ani da Hadisai da suke tabbatar da hakan.
  Kalubalantar ciwo bashi don aikin jirgin kasa a birnin Kano
  Abu na farko da ya fara kawo rashin jituwa tsakanin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da gwamnan Kano Abdullahi Umar ganduje shi ne kalubalantar matakin gwamnati na shirin karbo bashi don aikin jirgin kasa a cikin gari.
  A matsayinsa na masanin tattalin arziki, Sarkin na Kano ya ce babu wani alfanu da za a samu idan aka ciyo bashi domin aikin babu wata riba da Kano za ta samu da shi.
  Wannan kalami ya fusata gwamnatin Kano, abin da ya sa aka fara takun-saka, kuma dangantaka ta fara yin tsami.
  Lamarin ya kai ga yunkurin sauke Sarki daga sarauta da kuma kaddamar da bincike kan zargin kashe kudin masarauta ba bisa ka’ida ba.
  Wasu manya da suka hada da mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo da Alhaji Aliko Dangote sun shiga tsakani domin sasanta gwamnan Kano da Sarkin Kano.
  Shigar tasu ta sa majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da binciken da ta fara kan masarautar Kano.
  Ita ma hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta dakatar da binciken da ta fara kan asusun masarautar ta Kano .
  Zargin goyon bayan PDP a zaben gwamna na 2019
  Bayan kammala zabukan shekarar 2019, an bude wani sabon shafi na takun-saka tsakanin Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi, lamarin da ya yi kamarin da ba a taba zaton zai yi ba.
  Gwamnan Kano da magoya bayansa sun zargi Sarki Sanusi da goyon bayan dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamna.
  Sun yi zargin cewa ya fito fili ya yaki Ganduje, kuma ya yi amfani da kudinsa wajen yi wa dan takarar gwamnan na jam’iyyar PDP yakin neman zabe, sai dai sarkin ya musanta wannan zargi.
  Wannan zargi ya janyo gagarumar baraka tsakanin shugabannin biyu, lamarin da ya kai ga gwamnatin na yunkurin tube sarkin.
  Sai dai shiga tsakani da wasu manya suka yi ya sa gwamnati ta sassauto, to amma ta raba masarautar Kano gida biyar , inda ta kirkiri karin masarautu hudu da za su yi gogayya da Sarki Sanusi.
  Haka kuma, an rage yawan fadin masarautar Kano zuwa kananan hukumomi 10 daga 44, sannan aka mayar da mafi yawan hakiman masarautar zuwa wadancan sabbin masarautun.
  Masu zabar sarkin Kano sun kalubalanci matakin a kotu , sai dai wasu na ganin tamkar sarki Sanusi ne ya kai karar gwamnatin Kano.
  Wannan takaddama ita ce mafi girma cikin wadanda Sarkin Kano ya taba shiga a tsawon rayuwarsa, kasancewar ba a kansa kawai lamarin ya tsaya ba, ya shafi gwamnati, da jama’ar da ke karkashinsa da gadon sarautarsa da tarihi da kuma al’ada.
  Har yanzu ana zaman ‘yar marina tsakanin manyan shugabannin na Kano biyu.
  A yanzu dai wasu manyan arewacin Najeriya sun shiga tsakani da yunkurin sasanta Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi.
  Abin zuba ido a gani shi ne ko a wannan karon ma Sarki Sanusi zai tsallake fushin ‘yan siyasa a kan sauke amawalinsa, ko kuwa yaki zai ci rawaninsa?

  Rahoton BBC Hausa

  Turawa Abokai

  2 Sako

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan