Nasarori Da Ƙalubalen Da Ilimi Ya Fuskanta A Kano A 2019

122

Babu shakka, shekara mai ƙarewa ta 2019 ta haifar da wasu manyan al’amura a ɓangaren ilimi a jihar Kano.

Batutuwa kamar cin zarafi ta hanyar lalata a makarantun gaba da sakandire, bayyana ilimi kyauta kuma wajibi da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi da kuma kawar da bambancin da ake nunawa tsakanin masu Shaidar Karatu ta Babbar Difloma ta Ƙasa, HND da masu Shaidar Digiri da gwamnatin jihar Kano ta yi su ne suka mamaye tattaunawar da al’umma ke yi a ɓangaren na ilimi.

Ga wasu daga cikin batutuwan da majiyarmu ta tsakuro:

Cin Zarafi Ta Hanyar Lalata A Manyan Makarantu
Ɗaliban manyan makarantu da dama na Kano sun bayyana irin raɗaɗin cin zarafi ta hanyar lalata da suke fuskanta daga hannun ma’aikata, musamman malamai, waɗanda ke aiki a makarantun da abin ya shafa.

A watan Agusta, wata Kotun Majistire ta aika da Mataimakin Shugaban Makarantar Nazarin Fasahar Kiwon Lafiya dake Bebeji zuwa gidan yari na tsawon kwana biyar bisa zargin sa da cin zarafin wata ɗaliba mai aure ta hanyar lalata.

Wanda ake zargin, Mas’ud Abdullahi, wanda ya kammala karatunsa na Digirin Digir-gir, PhD, kuma yana dab da fara aiki da Jami’ar Gwamnatin Tarayya, Dutse, a matsayin malami, ana zargin sa da neman yin lalata da ɗalibar don ya ba ta maki, duk da cewa ya san tana da aure.

An gurfanar da Mista Abdullahi a gaban alƙalin Kotun Majistire, Aminu Fagge, wanda daga bisani ya ba shi beli, ya kuma ba shi Katinsa na Shaidar Aiki da motarsa, waɗanda aka ƙwace a matsayin hujjoji.

Amma kotun ta yi watsi da buƙatar bayar da wayar wanda ake zargin, tana mai cewa wayar na ƙunshe da hujjar saƙonnim soyayya waɗanda Mista Abdullahi ya aika wa ɗalibar.

Haka kuma, wani malami mai suna Ali Shehu wanda ke aiki a Makarantar Fasaha dake Ƙarƙashin Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, ya zo hannu a yayin wani samame, inda aka gano ya riƙa sanya ‘yan yatsunsa a al’aurar ɗalibarsa, wadda ya so ya kwanta da ita.

An gurfanar da Mista Shehu, ɗan shekara 36 ne a gaban Babbar Kotun Majistire ta Kano, bayan nan kuma kotun ta aika da shi gidan yari bayan ya amsa tuhumar cin amana da cin zarafi ta hanyar lalata, laifukan da suka saɓa da Sashi na 95 da 98 na Kundin Dokokin Penal Code.

Amma Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kanon ta nesanta kanta da wancan ma’aikaci da ake zargi.

Da yake mayar da martani ga al’amarin, Magatakardar Makarantar, Ado Mohammadu, ya bayyana kaɗuwa bisa faruwar lamarin, kuma ya faɗa wa manema labarai cewa wanda ake zargin ba ma’aikaci makarantar ba ne.

Magatakardar ya ce an turo Mista Shehu ne daga Ofishin Shugaban Ma’aikatan Jihar Kano a matsayin ma’aikaci wucin gadi a Makarantar Kimiyya da Fasahar.

Kwankwaso Ya Ba Ɗalibai 370 Masu Shaidar Karatun Digiri Maidaraja Ta Ɗaya Tallafin Karatu Zuwa Kasashen Waje

Gidauniyar Kwankwasiyya Development Foundation a Kano ta bada tallafin karatu zuwa ƙasashen waje ga ɗalibai 370 da za su yi digiri na gaba da na farko a jami’o’i a Indiya da Sudan.

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ya kafa wannan gidauniya, kuma tsohon gwamnan jihar Kano, ya bayyana haka a yayin wani taron ban-kwana da aka shirya wa ɗaliban da suka amfana da tallafin a Kano.

Ya ce gidauniyar ta biya dukkan kuɗaɗen karatun ɗaliban da suka haɗa da kuɗin ɗaukar karatu, kuɗin ɗakuna, kuɗaɗen ɓatarwa da kuɗaɗen dawowa.

Jami’ar Yusuf Maitama Sule Ta Kano Ta Yi Bikin Yaye Ɗalibai Karo Na Farko

A ƙalla ɗalibai 80 ne suka kammala karatu da Digiri Maidaraja Ta Ɗaya daga Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta Kano, YUMSUK, lokacin da jami’ar ta gudanar da bikin yaye ɗalibanta na farko, na biyu da na uku a haɗe a birnin Kano.

A lokacin bikin, ɗalibai 755 sun kammala karatu da Digiri Maidaraja ta Biyu ta Sama, ɗalibai 1,309 sun samu Digiri Maidaraja ta Biyu ta Ƙasa, yayinda ɗalibai 312 suka fita da Digiri Maidaraja ta Uku, daga cikin jimillar ɗalibai 2,456.

Haka kuma, ɗalibai 527 sun kammala a shekarar karatu ta 2015/2016 , 693 sun kammala a shekarar karatu ta 2016/2017, yayinda 1,236 suka kammala a shekarar karatu ta 2017/2018.

Ɗaliban Kano Masu Nazarin Likitanci Sun Shiga Halin Ni ‘Yasu A Indiya Bisa Rashin Biyan Kuɗin Makaranta Miliyan N22.

A watan Fabrairu, Ɗaliban Kano 14 Masu Nazarin Likitanci a Indiya waɗanda gwamnatin jihar Kano ta ɗauki nauyinsu sun fuskanci barazanar kora biyo bayan gazawar da gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta yi na biya musu kuɗin makaranta da suka kai naira miliyan N22 ($59,200).

Ɗaliban da suka shiga halin ni ‘yasun suna daga cikin ɗalibai da yawa da gwamnatin tsohon gwamna, Rabi’u Musa Kwankwaso ta fitar da su waje don karatu.

Ɗaliban 14 masu karatu a Institute of Medical Science and Research Centre, India, SSIMS and RC, Davanagere, sun faɗa cikin matsala ne lokacin da rahotanni suka ce gwamnatin jihar Kano ta ƙi biyan kuɗin makarantarsu.

Jami’ar Kano Ta Doke UNN da Yaba Tech A Gasar Rubutun Zube Ta Ƙasa

Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano dake Wudil, KUST,Wudil, ta yi nasara a Gasar Rubutun Zube na Kimiyya da Fasaha ta Ƙasa, NESTEC, inda ta doke Jami’ar Najeriya ta Nsukka, UNN, wadda ta yi ta biyu, da Kwalejin Fasaha ta Yaba, wadda ta yi ta uku.

Ganduje Ya Bayyana Ilimi Kyauta Kuma Wajibi

A watan Mayu, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ilimin firamare da na sakandire ya zama kyauta ga dukkan yaran da ya kamata a ce suna makaranta a jihar.

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a jawabinsa na amsar shugabanci jim kaɗan bayan an rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar Kano a karo na biyu.

Ya yi alƙawarin cewa daga yanzu ilimin firamare da na sakandire ya zama kyauta kuma wajibi ga dukkan yaran da ya kamata a ce suna makaranta a Kano.

A ta bakinsa, ilimin gaba da sakandire ma ga ɗaliban Kano shi ma za a yi rangwame a kai.
Kano Ta Kawar Da Bambanci Tsakanin Masu Digiri Da Masu HND

Wani ci gaba da za a iya tunawa da shi shi a 2019 shi ne kawar da bambanci tsakanin masu Shaidar Karatun Digiri da masu Shaidar Babbar ‘Diploma’ ta Ƙasa, HND a jihar Kano.

Gwamna Ganduje ya sanar da haka ga ma’aikata a yayin bikin Ranar Ma’aikata a Filin Wasa na Sani Abacha.

A cewar Gwamna Ganduje, gwamnatinsa za ta ci gaba da ba jin daɗin ma’aikata da ma sauran al’ummar jihar fifiko.

Dama tuni Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, NLC, Reshen Jihar Kano, Ado Minjibir, ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta riƙa biyan alawus-alawus ga ma’aikatan manyan makarantun jihar kamar yadda ake biyan abokan aikinsu dake ƙarƙashin makarantun Gwamnatin Tarayya.

Ganduje Ya Biya Bashin Biliyan N2 Ga Ɗaliban Kano A Jami’ar Sudan

Gwamnatin jihar Kano ta biya bashin fiye da biliyan N2 na bashin kuɗin makaranta ga ɗalibanta dake karatu a Jami’ar El-Razi dake Sudan.

Gwamnatin jihar ta ce gwamnatin tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ce ta tara wannan bashin.

Gwamna Ganduje ya ce ya gaji ɗaliban ne daga gwamnatin da ta gabata da tarin bashi da ba a biya ba.

Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta biya fiye da miliyan N300 ga Jami’ar Cyprus don ba ɗaliban da jihar ta ɗauki nauyin karatunsu damar kammala karatunsu.

An Ɗaga Darajar Makarantar Koyon Aikin Jiyya Zuwa Makaranta Mai Bayar Da Digiri

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi wa dokar da ta kafa Kwalejin Koyon Aikin Jiyya da Ungozoma kwaskwarima don ba kwalejin damar fara bada Shaidar Karatun Digiri, Diploma da Babbar Shaidar Diploma ta Ƙasa, HND.

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Alhaji Labaran Abdul-Madari ya ce kwalejin, wadda a da takardun shaida kawai take bayarwa, a yanzu za ta riƙa bayar da Digiri da sauran shaidun karatu.

A ta bakinsa, dokar za kuma ta ba kwalejin damar ɗaukar ɗalibai masu ‘credits’ biyar a Turanci, Lissafi da Biology, musamman waɗanda suke a ƙauyuka don ba su horon shekara ɗaya kan Aikin Jiyya da Ungozoma.

Ya bayyana cewa wannan zai sa ɗalibai daga ƙauyuka damar samun Ilimin Jiyya da Ungozoma, ta haka za su iya taimaka wa wajen rage yawan mace-macen mata da ta jarirai yayin haihuwa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan