Tabbas tsarin Npower wanda yake daya ne daga cikin tsarukan da ake kiransu da ‘Social investment programmes’ ya samar da dubunnan matasa aikin yi a kasar Najeriya.
Kamar yadda yake a bayyane, tsarin ya bawa matasa dubu dari biyar (500,000) aikin wucin-gadi na shekara biyu a fadin Najeriya.
Wadannan matasa an daukesu ne a kashin farko wanda yake dauke da mutum dubu dari uku (Batch A, 300,000), sannan sai kashi na biyu wanda yake dauke da matasa dubu dari biyu (Batch B, 200,000)
Rukuni na farko na tsarin ya cinye shekara ta uku a cikin tsarin a karkashin abuda ake kira da ‘Enhancement’ shi kuma rukuni na biyu yana da ragowar watanni kafin ya cika shekara biyu ma.
A kwanakin baya, an samu maganganu iri iri akan mayar da wadannan matasa ‘yan sandan cikin alqarya (Community police) amma abun bai yiwu ba. Wata maganar kuma tazo da zancen basu aiki a gwamnati da ma’aikatu masu zaman kansu. Wanda hakan yasa da yawa daga cikin matasan sun canza shirinsu.
Labudda, a cikin matasan akwai wadanda suka yi aure saboda sun ci auren tuntuni. Don duk mutumin da ya shiga shekarun aure baya hango matsalar da zai shiga bayan yayi saboda tarihi ya nuna mana cewa wasu daga cikin manyan Najeriya sun yi aure basu da sana’a ma.
Peter Murdock yace, aure al’adar duk duniya ne, a cikin kowacce al’umma za a iya samunsa. Tana da aiki, ko bata dashi. A tunanina, dan Npower yafi dan jagaliyar siyasa aikin yi amma gasu muna ganinsu da aure. Saboda haka, ni ban ga laifin dan Npower dan shekara 30 zuwa 35 ba don yayi aure. Tabbas, sallamar wadannan matasa zata janyo mace-macen aure da laifuka saboda cikin fatara da talauci zasu shiga
Muna godiya ga gwamnati data samar da tsarin, sannan muna bata shawara cewa, karshen tsarin yafi komai amfani tunda an samar dashi ne don ya samar da karshe mai kyau (Basic outcome/positive impacts).
Allah ya jiyar damu alheri a Najeriya.

Daga Mustapha Soron Dinki
Yan batch A 200,000 ne, ba 300,000 ba
Yan batch B 300,000 ne, ba 200,000 ba
Allah ya taimaka