Itacen dalbejiya ko kuma dogon yaro ko ‘Neem tree’ a turance tana da daci amma tana da matukar amfani ga jikin mutum.
Ga wasu hanyoyi da amfani da dalbejiya ke yi a jikin mutum:
- Ganyan dalbejiya na kare mutum daga kamuwa da cutar bugawar zuciya musamman idan aka dafa ganyen ana shan ruwan kamar shayi.
- Ganyen dalbejiya na taimakawa wajen tacewa da tsaftace jinin mutum a jikin sa.
- Ganyen na maganin cutar zazzabin cizon sauro da Typhoid.
- Yana kuma maganin cutar ciwon ciki musamman idan cikin mutum ya murde saboda wani abincin da aka ci.
- Ganyen dalbejiya da man shi na gyara fatar jikin mutum.
- Ganyen na maganin sanko, magance amosanin kai da kuma sanyawa gashi ya yi tsaho, ta hanyar shafa man dalbejiya a ka.
- Ana iya amfani da man dalbejiya a matsayin dabarar bada tazarar iyali.
- Ganyen na kawar da cutar daji musamman dajin dake kama nono, ‘ya’yan maraina sannan yawan amfani da ita na hana kamuwa da cutar.
- Ganyen na maganin cutar gyambon ciki wato ‘Ulcer’ da kuma rauni a jiki.
- Yana rage kiba a jiki musamman ga masu fama da ita.
- Yana warkar da ciwon gabobi da ciwon kai.
- Yana kare mutum daga kamuwa da cutukan da ake samu ta hanyar yin juma’i
- Warkar da kuturta.
- Yana maganin ciwon ido.
- Yana maganin guba da ake samu daga jikin dabba kamar cizon cinnaka, maciji da sauransu.
- Ganyen na maganin kwari musamman wadanda ke lalata amfanin gona.



Turawa Abokai