Yin Azumi Sau 2 A Kowanne Mako Ya Na Ƙara Tsawon Rai – Binciken Masana

86

Malaman Kimiyyar Amurka sun bayyana cewar sakamakon wani bincike da suka gudanar ya bayyana yin azumi a kowanne mako ko kuma kame baki daga barin cin abinci na wasu awanni a rana na kara tsawon rayuwa tare da riga-kafin cututtuka da dama.


Sakamakon binciken da aka buga a mujallar Likitanci ta New England ya ce cin abinci a cikin awanni 6 zuwa 8 sannan a kame a awanni 16 zuwa 18 na kowacce rana na kara tsawon rai, rage karfin harbawar jini da riga-lafin cututtuka da dama.


Rahoton ya ce yin azumi a kwanaki 2 a kowanne mako na iya maganin cututtukan zuciya, kiba da ciwon sukari a saboda haka ake shawartar mutane da su yi hakan.


Binciken da aka gudanar a kan mutane da dabbobi ya nuna yin azumin na daidaita yanayin sarrafuwar abinci da gudanar jini a jikin dan adam, sannan yana sabunta lafiya.


Haka zalika na magance kwayoyin Insulin na jikin mutum wanda hakan abu ne mai kyau ga masu ciwon sukari.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan