Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bada umarnin cewa daga yanzu ba wani minista da zai yi tafiya zuwa ƙasashen ƙetare fiye da sau biyu a cikin wata uku.
Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, wanda ya bayyana wannan umarni, ya ce daga yanzu, jami’an gwamnati da suke ƙasa da muƙamin minista za a riƙa ba su hadimai ne kaɗan.
“Banda haka kuma, ba wani minista da zai yi tafiya ya bar Najeriya da hadimai fiye da huɗu, waɗanda suke da muhimmanci a tafiyar”, in ji Mista Mohammed.
Turawa Abokai