Sama Da Mata Ɗari Sun Bayyana Aniyarsu Ta Auren Babangida

229
27 Feb 1990, Paris, France --- Nigerian President Ibrahim Babangida arrives in Paris for a four-day official visit to France. --- Image by © Reuters/CORBIS

Bayan wallafa labarin tsohon Shugaban Ƙasa Ibrahim Badamasi Babangida na neman Matar da zai Aura, yanzu haka sama da Mata 100 ne suka aiko mana da Saƙon suna son shi tsakani da Allah, kuma suna neman taimako a haɗasu da shi.

Aa ƙarshe muna tunanin wallafa sunayensu da hotunan su harma da lambar wayar su, domin neman dacewa da auren tsohon shugaban kasar Dattijo mai shekaru kusan Tamanin.

Indai jama’a basu manta ba a makon da ya gabata ne Tsohon Shugaban mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mainritaya) ya sanar da cewa yana neman sabuwar matar da zai aura.

Da yake bayanin irin macen da za ta dace da shi a wannan matakin na rayuwarsa, IBB ya ce ba zai auri mace da ke cikin kuruciyan ta ba domin hakan zai zama matsala ga matar da kuma kansa.

Da yake magana da jaridar ‘The Sun’, tsohon Shugaban kasa ya bayyana fargabar sa cewa sabuwar matar da za ta yi rayuwa da shi ba za ta cike gurbin tsohuwar matarsa marigayiya Maryam ba

Daga Shafin Muryar Ƴanci

27 Feb 1990, Paris, France — Nigerian President Ibrahim Babangida arrives in Paris for a four-day official visit to France. — Image by © Reuters/CORBIS
Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan