Ganduje Ya Fara Biyan Ma’aikatan Kano Mafi Ƙarancin Albashi

171

Gwamnatin jihar Kano ta fara biyan ma’aikatanta mafi ƙarancin albashi.

Dama tun a wata tattaunawa da majiyarmu, Shugaban Hukumar Sasantawa Tsakanin Gwamnati da Ma’aikata, JNC, Hashim Saleh, ya ce gwamnatin jihar Kano za ta fara biyan mafi ƙarancin albashi daga 31 ga Disamba, 2019.

Wasu ma’aikata da suka tattauna da majiyarmu bisa sharaɗin kar a bayyana sunayensu sun ce sun lura da ƙari a albashinsu.

Wata malamar sakandire da take kan Matakin Albashi Maidaraja ta 6, ta ce ta samu ƙarin naira N12,003, yayinda abokiyar aikinta dake Matakin Albashi Maidaraja ta 7 ta samu ƙarin N10,286.

Haka kuma, wani ma’aikaci shi ma da yake kan Matakin Albashi Maidaraja ta 9, ya ce ya ga ƙarin naira N9,000, yayinda wani da yake kan Matakin Albashi Maidaraja ta 8 ya ce ya samu ƙarin naira N3,400 a albashinsa.

Haka kuma, wani jami’in Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano, ya faɗa wa wakilin majiyarmu cewa an biya shi naira N25,000, maimakon N15,000 da ake biyan sa a baya.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan