Yadda Isma’il Tangalash Ya Lashe Kyautar Gwarzon

1080

Shahararren mai gabatar da labarin wasanni kuma masani aharkar wasanni bugu da kari mai fashin baki a wasanni daban-daban wato Isma’il Abba Tangalash ya lashe kyautar gwarzon mai gabatar da shirin labarin wasanni na Arewacin Najeriya.

Inda arewacin kasar yake dauke da jahohi 19 kuma ya doke abokan takarar sa na jahar Gombe da kuma na jahar Kwara.

Wannan kyauta da Tangasports International ya lashe kyauta ce wadda daga cikin kyaututtuka na Arewa Sports Personality Award (ASPA) wato mutanen da sukayi bajinta a jahoshin Arewacin Najeriya abangaren wasanni.

Wannan kyauta da Tangalash ya lashe bata rasa nasaba da irin yadda yake saka salo idan yana gabatar da shirin labarin wasanni da kuma isar da sako da zafinsa ya isa kunnuwan masu sauraro acikin jahar Kano da sauran jahoshin kasarnan wani lokacin harma da kaaashen waje musamman idan yana yiwa sashen Hausa na gidajen rediyoyin BBC da France International da DW ta Jamus fashin baki, haka akwai gudun mawa dayake bayarwa a rubuce ta harsuna daban daban musamman yaren Turanci dana Hausa, haka Tanga bai tsaya nanba harma a gidajen Telebijin da dama yana bayar da gudun mawa kamar Arewa 24 da ARTV.

Ayayin tattaunawa da jaridar Labarai24 tayi da Tangalash yace “Inayiwa Allah godiya dayabani damar lashe wannan kyauta, sannan ina godiya ga masoya da suka zabeni, sannan ina godiya ga ‘yan uwa abokan aiki marubuta Iabarin wasanni duba da cewa ko yaushe kanmu a hade yake”

Daga karshe Isma’il Abba Tangalash ya nuna farin cikinsa dangane da wannan kyauta daya lashe ta gwarzon mai gabatar da shirin labarin wasanni na Arewacin Najeriya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan