Alƙawura 10 Da Buhari Ya Ɗauka A Sabuwar Shekara 2020
Shugaba ƙasa Muhammadu Buhari ya dauki wasu sababbin alkawurran da ya sha alwashin cikawa a cikin shekarar 2020.
Cikin jawabin da ya gabatar ranar Laraba a ranar 1 Janairu, 2020, Buhari ya yi dogon jawabin da ya tunatar da ‘yan Najeriya dajin da gwamnatin sa ta keto, wasu nasarori da aka samu da kuma kalubalen da ke Gavan gwamnatin sa.
- Zan gina titina 47 a fadin kasar nan, wadanda za a kammala aikin su tsakanin 2020 zuwa 2021.
- Zan gina manyan gadoji masu tarin yawa a kasar nan cikin 2020, ciki har da ci gaba da ginin Gadar Kogin Neja Sashe Na 2.
- Zan gina rukunin gidaje masu tarin yawa cikin 2020, har rukuni-rukuni 13.
- Zan kaddamar da gaggarimin Shirin Inganta Noman Karkara wanda za a yi a Kananan Hukumomi sama da 700. Shirin zai dauki shekara uku ana gudanar da shi domin ya kankama ka’in-da-na’in.
- Zan kaddamar da shirin samar wa makiyaya kadadar kiwo a Jihar Gombe, mai fadin hekta 200,000.
- Zan horas da ma’aikata 50,000 a cikin 2020 domin kara yawan wasu 7,000 da ake da su da suka samu horo.
- Nan da watanni uku zan fara aikin titin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano.
- Zan bada dama masu jari su sa hannu wajen inganta samar da wutar lantarki, ta yadda za ta kara inganta sosai.
- Zan fara ginin Tashar Hasken Lantarki ta Mambilla nan da watanni uku.
- Zan samar wa mutane milyan 100 aiki, nan da shekaru 10.

Turawa Abokai
Allah ya yarda amin