Wani Kwamishina Ya Bayyana Aniyarsa Ta Gadon Kujerar Ganduje

256

Kwamishinan ayyukan jihar Kano wato Muaz Magaji dan sarauniya ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Kano a shekarar zabe ta 2023.

Muaz Magaji ya bayyana hakan ne a mazabarsa ta Danguguwa da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa lokacin da jama’ar mazaɓar su ka shirya masa liyafar tayashi murna tare da adduar samun nasarar shiga ofis.

Injiniya Muaz Magaji ya bayyana cewa idan Allah ya bashi nasarara zama gwamnan Kano to babu shakka zai baiwa kowa hakkinsa tun daga kan ƴan jamiyyarsa ta APC dama jamiyyar adawa.

Ba wannan ne karon farko da Muaz Magaji ya bayyana aniyarsa ta yin takarar gwamnan jihar Kano, ko a shekarar 2015 sai da ya nuna sha’awar yin takarar a Jam’iyyar APC.

Taron liyafar dai ya samu halartar Limamai da Dagatai da masu Unguwanni da kuma ƴan siyasa da ke fadin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa.

Daga Shafin Baka Noma

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan