‘Abubuwan Al’ajabi’ Game Da Marigayi Mamman Shata

33

Mamman Shata, wanda aka haifa a 1923 a yankin ƙaramar hukumar Musawa ta jihar Katsina, ya rasu ranar 18 ga watan Yuni, 1999.

Shata, wanda shahararren mawaƙin Hausa ne yana da waƙoƙi da aka naɗa masu tarin yawa. Sau da yawa kalangu suna raka wa waƙoƙinsa baya.

Ya shafe fiye da shekara 50 yana yi Hausawan Najeriya da na wasu sassan Afirka waƙa da ma waɗanda ba Hausawa ba.

Mahaifiyar Shata, Lariya, Bafulatana ce daga ƙabilar Fulani da ake kira Fulata-Borno, Fulanin da suka yi hijira daga Daular Borno bayan Jihadin Fulani na 1804, suka bazu a wasu sassan ƙasar Hausa.

Ta haɗu da mahaifin Shata, Ibrahim Yaro, lokacin da ta je ziyarar wani ɗan uwa. A sakamakon haka, suka yi aure, suka haifi ‘ya’ya uku. Yaro, Mamman Shata da ‘yar uwarsa, Yalwa.

Ga wasu bayanai a ƙasa game da Shata waɗanda wata ƙila ba ku san su ba:

Shata Ya Samu Laƙabinsa Ne Na ‘Shata’ Daga Wani Mutum Da Ake Kira Baba Salamu, Ɗan uwansa

A lokacin da Shata yake saurayi, ya riƙa siyar da goro, bayan ya siyar sai ya raba ribar ga mutane da ya haɗu da su a hanyarsa ta zuwa gida ko kuma a kasuwa, sai ya dawo ba komai. Idan aka tambaye shi me ya yi da ribar da ya samu, sai ya bada amsa: “Na yi shata da su, ma’ana, na bada su. Sakamakon haka, sai Baba Salamu ya riƙa kiran sa Mai-Shata, wato wanda yake bada ribarsa.

Shata Ya Je Aikin Haji Sau Ɗaya A Rayuwarsa

Duk da dai ya ziyarci ƙasashen duniya da dama kamar Birtaniya, Faransa da Amurka, Shata ya je Haji sau ɗaya ne a rayuwarsa. Rahotonni sun ce wani shahararren ɗan kasuwa a Kano, Haru Dan-Kasim ne ya biya wa Shata aikin Hajj a 1954.

Shata Ɗan Siyasa Ne, Ya Riƙe Muƙaman Siyasa Da Yawa

Shata ya yi siyasa sosai a lokacin da yake raye. Yawancin siyasarsa ta ‘yan juyin juya hali ce koda yake iyayensa a siyasa su ba haka suke ba.

A shekarun 1970, ya ci zaɓe, inda ya zama kansila a ƙaramar hukumar Kankiya, a tsohuwar jihar Kaduna. A Jamhuriya ta Biyu, (a ƙarshen 1980), ya shiga jam’iyyar GNPP, sannan ya koma jam’iyyar masu ra’ayin mazan jiya, NPN.

A Jamhuriya ta Uku, an zaɓe shi a matsayin Shugaban Jam’iyyar SDP a ƙaramar hukumar Funtuwa, muƙamin da aka tsige shi saboda halayyarsa ta son juyin juya hali da kuma rashin jituwa da uban jam’iyyar a jihar Katsina, Manjo Janar Shehu Musa ‘Yar Aduwa.

Baiwar Shata Ta Waƙa Ta Fara Bayyana Tun Yarintarsa

Shata ya fara waƙa da sauran matasa a ƙauye a dandali bayan Magriba. Baiwarsa ta girma har ta goge ta sauran yara mawaƙa. Amma ba yana yi ba ne a lokacin don a ba shi kuɗi. Kawai dai sana’a ce ta yara.

Mahaifin Shata Bai So Ɗansa Ya Zama Makaɗi Ba

Ibrahim Yaro bai so a ce ɗansa ya zama makaɗi ba saboda abinda kowa ya yi imani da shi cewa kiɗa ko yabo wani nau’i ne na roƙo ko maula. Mahaifinsa, kasancewar sa Bafulatani, ya sa ran Shata zai zama manomi ko ɗan kasuwa. Dagewar da Shata ya yi ta zama makaɗi ta zama wani abu kamar tawaye.

Shata Ya Shafe Shekara 30 Yana Sharafi, Ya Zama Ɗaya Daga Cikin Mawaƙan Hausa Da Aka Daɗe Ana Sauraron Su A Duniya

A 1952, shahararsa ta fito fili a Kano bayan ya yi waƙa a wani Bikin ‘Ya’yan Sarki, inda wasu ‘ya’yan Sarki 12 suka yi aure. Masanin tatsuniya ne da ake ganin girman sa. Ya yi kusan shekara 50 zuwa 60 yana waƙa. Shata bai iya tuna waƙoƙi nawa ya yi ba. Da yawa daga cikin waƙoƙinsa, musamman waɗanda ya yi da ƙuruciya, ba a iya naɗar su ba.

Shata Ya Yi Wa Abubuwa Da Yawa Waƙa

Shata ya yi waƙe kusan kowane abu a ƙasar Hausa: rana, aikin gona, al’ada, addini, tattalin arziƙi, siyasa, aikin soja, tarbiyya da ladubba, dabbobi, kasuwanci da sauransu.

Shata Ya Samu Kyaututtuka Da Dama A Gida Da Waje

Shata ya samu kyaututtuka da yawa, waɗanda suka haɗa da na Gwamnatin Tarayya (wadda ta ba shi lambar MON), da wadda Ƙungiyar Mawaƙa ta Ƙasa, PMAN ta ba shi, da ta gwamnatin jihar Kano, da ta Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya, da ta Jami’ar California, Los Angeles da Digirin Digir-Gir na Girmamawa da Jami’ar Ahmadu Bello ta ba shi bisa gudunmawarsa wajen ci gaban ƙasa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan