Rake sarkin zaƙi, duk yadda ka kaɗa cikin faɗin arewacin ƙasar nan ka ga rake. Kuma yana da muhimmanci ga lafiyar ka bayan ka more da ɗankaran zaƙi, sai kuma ka samu tallafi daga rake cikin ƙanƙanin kuɗi.
Shifa rake ya na ɗauke da sinadaran antitoxin da bitamin C da ke haɓaka garkuwar jiki wajen yaƙar cututtuka, kariya daga ruɓar haƙora, kariya daga cutar yoyon fitsari da ciwon ƙoda, na dauƙe da; calcium, iron da patassium wanda ke samar da kuzari domin aikin yau da kullum. Kar ka manta rake ne abun da yafi goge maka hanta fiye da kowane magani, gashi ana amfani da raken wajen hada abinci mai suna ‘jaundice’ wadda ke ba da kariya daga ciwon sankara.
Shifa rake yana agaji ɓangaren rage ƙiba ko teɓar jiki, domin samun rage jiki sai ka tauna rake ka mori zaƙin.
Za a iya tafasa ruwan rake domin haɗa waɗansu kala-kalar abinci masu daɗin ɗanɗano.
Ga yadda za a haɗa abin shan rake
Kayan da ake buƙata wajen haɗa abin shan rake.
Ɓararran rake
Ruwan lemo
Ina ka so sai ka haɗa da
Strawberry
Citta
Kwakwa
Mangwaro
Yadda za’ayi abun shan rake
Haɗa duk waɗannan kayayyaki cikin abun malkaɗe (blender).
Juye malkaɗanɗun kayan a kwano (mazubi)
Tace malkaɗan raken tare da ƙanƙara.
Ba buƙatar a sa masa madara, sukari ko abun da zai sa shi ya jima ba tare da lalacewa ba (preservetive). Kana buƙatar abun sha na rake a irin waje mai zafi, domin nisahɗi ko more abun sha mai ƙunshe da sanadarai masu amfani.
Amfanin Rake Da Ya Kamata Ka Sani A Sabuwar Shekarar 2020
Turawa Abokai